Daga MUKHTAR YAKUBU
A kwanakin baya ne mai bai wa Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf shawara Hajiya Aina’u Ade ta gudanar da taron bayar da tallafi ga mabuƙata musamman dattawan cikin Kannywood, in da a wajen taron aka ga ta bayar da wani ƙunshin kuɗi ga mahalarta taron, baya ga haka kuma aka bi waɗansu har gida wato marassa lafiya aka kai musu, wasu kuma suka je ofishinta suka karbi nasu.
Ganin yadda rabon kuɗin ya kasance ne wakilinmu ya ji ta bakin Aina’u Ade dangane da wannan rabon kuɗin da ta yi. Don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance:
MANHAJA: Bayan wannan taro da kika shirya a ‘yan kwanakin nan mun ga kin fito da wani tsari na bayar da tallafin kuɗi, ko za ki yi wa masu karatun mu bayani dangane da wannan tsarin naki?
AINA’U ADE: To kamar dai yadda aka sani ni ce mataimakiya ta musamman ga Gwamna Abba Kabir Yusuf a kan Masana’antar Kannywood, don haka duk wani abu da ya shafi bayar da taimako ga mutanen Kannywood zan tsaya na ga an samar da shi, saboda ni wakiliyar Gwamna ce a cikin masana’antar, don haka ni ce idon sa , don haka duk wani abu da muka san ana buƙatar a samar da shi za mu isar da shi ga Gwamna, kuma da yake shi Gwamna mai adalci ne, wanda yake son ya ga ya taimaki mutane don haka duk abin da na kai masa na buƙatar mu na san zai yi mana saboda karamcin sa.
Aƙalla daga shigar ki ofishin nan kin gudanar da ayyukan da suka kai nawa?
To da yake ka san ban daɗe da fara zuwa ofishin ba, amma dai ina zuwa na fara gabatar da ayyukan da suka kamata na yi. Matakin farko da na ɗauka, na ga akwai tsofaffin mu da yawa waɗanda a yanzu zamani ya zo da ba za su samu a saka su a fim ba, don haka ba su da aikin da za su yi ma ballantana su samu abin da za su gudanar da rayuwarsu.
To ni ina so na tsaya a kan irin waɗannan tsofaffin saboda ƙarfin su ya ƙare, idan har ba a tallafa musu da abin da za su ci ba da me za a tallafa musu. To lokacin da muka yi taro sun nemi a shirya musu wani taron bita, ta ƙarƙashin ofishina ko yadda za a samar musu da abin da za su yi ko kiwon Kifi da kaji a gida da makamantan su.
A yanzu kamar mun ga kin fara da bayar da tallafin kuɗi ko shi ma wani tsari ne na daban?
E. Wannan tsari ne na tallafin kuɗi na fara samar musu, ko da yake tun kafin azumi na nemar musu, wanda nake tunanin za a samu su yi amfani da shi da azumi, to Allah bai yi ba sai a yanzu aka samu. Kuma tallafi ne wanda na nema musu, kuma a yanzu kowa an ba shi kuɗi, kuma cikin yardar Allah mutane sun ji daɗi sun yi farin ciki, kuma kaima a kan idon ka ka ga yadda tsofaffin ‘yan fim da suka zo suka karɓi nasu ka ganni da Tahir Fagge, Kabiru Nakwango, da Bashir Nayaya. Kuma ko a jiya akwai mutanen mu da ba su da lafiya da muka bi su muka ba su. Kuma na kai kuka ga Gwamna Abba Kabir Yusuf cewa ya taimaka duk wani abu na buƙata idan ya taso za mu je mu same shi don ya taimaka, saboda tsofaffin nan namu shi ma na san yana son su.
Ko akwai adadin mutanen da aka ware na kuɗaɗen da za a bayar?
Gaskiya Babu wani adadi, ai duk abin da za ka yi a rayuwarka ka yi domin Allah, don haka ni duk wanda ya zo wajena lokacin da mutum ya zo in da rabon sa zai samu. Sai dai Gwamnan namu zan roka , a cikin adalcin sa, akwai wanɗada ba su samu ba, muna son a ba mu ko yaya mu ba su don su ma su ji daɗi a ran su, don a yanzu mutanen da suka samu sun kai dari da hamsin, akwai waɗanda aka bai wa dubu ɗari, wasu dubu ɗari da hamsin akwai masu dubu hamsin ma.
Wannan irin buri kike so ki cimma a matsayin ki ta mai ba gwamna shawara a kan Masana’antar Kannywood?
A gaskiya ina da bururruka da yawa, amma dai a bin da na sa a gaba a yanzu shi ne na ga na taimaki mutane, to da yake shi Gwamna abin da ya sa a gaba kenan, to zan so na ga na taya shi wajen taimaka wa jama’a.
Su ‘yan fim da suka samu tallafin, ko wanne kira za ki yi a gare su?
To kiran da zan yi shi ne, kada su yarda su raba kansu a kullum mu zama tsintsiya maɗaurin ki ɗaya. Sannan mu rinƙa yaƙar zuciyar mu da baƙin ciki, mu yarda Allah shi ne yake yin komai, a dalilin wanda Allah ya yi wa ni’ima idan ka taya shi murna sai ka ga ka samu komai. Muna fatan Allah ya shiga labarin mu, kuma a madadin ‘yan fim muna ƙodiya ga Maigirma Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa irin kulawa da yake bai wa ‘yan fim a kan duk wasu buƙatu na su Allah ya saka da alheri.
Madalla mun gode.
Ni ma na gode sosai.
