Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Samar da Zuba Jari ta Jihar Kano, Kan-Inɓest, ta yi fatali da wani rahoto da Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta fitar, inda ta ce jihar ta samu dala 120,000 ne kacal a cikin Kuɗaɗen Zuba Jari na ƙasashen Waje (FDI) a farkon shekarar 2025.
Rahoton wanda wasu sassan kafafen yaɗa labarai suka wallafa, ya bayyana cewa, jihohi 7 ne kawai suka ja hankalin ƙasashen waje a farkon shekarar 2025, inda Abuja da Legas ke kan gaba, yayin da wasu jihohi 30 ciki har da Kano suka kasa kataɓus.
Sai dai a wata sanarwa ɗauke da sa hannun kakakinta, Aminu Samɓauna a Kano a ranar Juma’a, hukumar ta bayyana cewa a cikin farkon 2025 kaɗai, Kano ta samar da FDI sama da dalar Amurka miliyan 22 na zuba jarin makamashin da za a sabunta, musamman a ɓangarorin da suka haɗa da iskas gas ɗin CNG da LNG.
A cewarsa, akwai wasu shawarwarin zuba jari a bututun mai da ke jiran amincewa, wanda ya zarce abin da Kano ta samar a farkon 2025 kaɗai.
Samɓauna ya ce, bayanan da waɗancan kafafen yaza labarai suka wallafa, dangane da NBS kuskure ne kuma bai kamata a yi la’akari da su ba.
“Abin mamaki ne a ga wata hukuma irin ta NBS, wacce kafafen yaɗa labarai ke dogaro da ita don samun ingantattun bayanai da za a iya tabbatar da su, ta fitar da bayanan da ba su dace ba ba tare da tuntuɓar jihohi don samun cikakkun bayanai ba,” inji shi.
Kakakin ya ƙara da cewa; “An tilasta mana mu magance wani gagarumin saɓani a cikin alƙaluman zuba hannun jari na ƙasashen waje (FDI) na jihar Kano a cikin farkon 2025, kamar yadda hukumar ƙididdiga ta ƙasa da sauran kafafen watsa labarai suka buga.
