
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Jihar Imo ƙarƙashin jagorancin Hope Uzodimma, ta dakatar da bukukuwan yaye ɗalibai a matakin nazare da ƙaramar sakandare duba da matsi da iyaye ke fuskanta yayin gudanar da su.
Kwamishinan Ilimi na jihar, Farfesa Benard Ikegwuoha a wata takarda ga iyayen yara, da makarantu ya sanar da haka.
A cewarsa, waɗanda suka kammala firamare da babbar sakandare ne kaɗai za a riƙa yi wa bikin yayewa bisa la’akari da dokar karatu ta 6-3-3-4, wadda ta rarraba matakan Ilimi.
Ya kuma ce, Ma’aikatar Ilimin makarantun firamare da sakandare tana aiki tuƙuru wajen samar da ilimi mai nagarta ga baki ɗaya ɗalibai a jihar.
Don haka, an rushe dukkan wani biki na nazare da ƙasa da haka ko ƙaramar sakandare a jihar duba da yadda ya ke haifar da matsin tattali akan da dama daga cikin iyayen.
Ya ƙara da cewa, bikin yaye ɗalibai mataki ne na nasara a ilimi ba gasar kuɗaɗe ba da ake nunawa a lokutan.
Bugu da ƙari, gwamnatin jihar ta haramta sabunta wa yara littafai a kowace shekara da makarantu ke umarta.
Akan haka ta bijiro da tsarin da ke nuna za a riƙa amfani da littafi har na tsawon shekaru huɗu kafin a sauya su, wato kenan ƴan gida ɗaya za su iya amfani da littafi ɗaya daga babba zuwa na ƙasa da shi don rage wa iyaye kashe wasu kuɗaɗe a kai.

