Adadin masu neman rijistar jam’iyya a Nijeriya sun kai 171

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Zaɓe INEC, ta ce adadin ƙungiyoyin siyasa da ke neman a yi musu rajistar jam’iyya sun kai guda 171 zuwa yanzu.

A sanarwar da ta fitar ta hannun babban jami’inta na wayar da kan masu zaɓe, Sam Olumekun a ranar Alhamis, inda ya ce daga lokacin da suka bada ba’asi a baya zuwa yanzu an samu ƙarin wasu guda 19 da ke neman a yi musu rajistar jam’iyya.

Lamarin da ya sa adadin ya kai 171 a shafin yanar gizo INEC da wasu kafafen yaɗa labarai.

A yanzu, INEC tana aiki kan tantance masu neman kafa jam’iyyun bayan ta gindaya musu wasu sharuɗɗa da za su bada damar tabbatar da su, kamar ya bayyana.

Ta kuma kiraye su da su ba ta lokacin a yayin da take aiki akan buƙatun nasu.

Kazalika, INEC ta nemi da su guji sauya tambarinsu, gajerun sunayensu, adireshi ko miƙa takardun neman rajista sama da sau ɗaya, lamarin da ka iya sa a ƙi tantance su.

By Babaji