Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan yayi wannan magana a garin Daura lokacin da ya halarci bikin sallar gani.
Bikin sallar gani,boki ne da masarautar Daura ke shirya wa a kowace shekara domin murnar zagayowar haihuwar Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama.
Malam Dikko ya sanar da cewa gwamnatin jihar za ta ɗaukaka wuraren tarihi kaman su Rijiyar Kusugu,katangar birnin Daura da sauran su,yi zuwa dai dai da wuraren tarihi da al’adu na ƙasashen duniya.
“Zamu ƙayata wuraren tarihi na jihar da za su kai ga janyo masu yawon buɗe idanu daga ƙasashen duniya wanda hakan zai bunƙasa tattalin arzikin jihar,”Inji Dikko.
Ya bayyana mahimmancin da gwamnatin sa ta ke bai wa masarautun gargajiya a jihar wanda har ta kai da ɗaga matakin albashi na hakimai zuwa mataki na 16 da na masu unguwanni.
Ya ce bikin sallah Gani ba wai bikin al’adun gargajiya bane “Rana ce ta tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama.
Sai yayi kira ga al’ummar Jihar Katsina za su zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya, a cewar sa mutumin Danja, Katsina, Daura, Malumfashi dukkan su addini da al’adar su ɗaya ne.
Gwamnan ya kuma yi kira a masu riƙe da sarakunan gargajiya da al’ummar jihar su ba gwamnatin goyon baya wajen samar da dawamammen zaman lafiya da kawo cigaban al’umma.
Ya jinjina wa Sarkin Daura bisa ƙoƙarin sa na raya al’adu da haɗa kan al’umma sa domin cigaban masarautar da Jihar Katsina baki ɗaya.
Muhimman mutane ciki da wajen Nijeriya da suka haɗa da jakadun ƙasashen waje suka halarci bikin na sallah Gani.
