UNICEF ta sha alwashin ci gaba da tallafa wa mata da ƙananan yara a Jigawa

Spread the love

Asusun kula da tallafawa ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, wato UNICEF, ta sha alwashin ci gaba da tallafawa Jihar Jigawa, duba da jajircewar gwamnatin Malam Umar Namadi wajen inganta rayuwar mata da ƙananan yara a faɗin jihar.

Wakiliyar UNICEF a Najeriya, Wafaa Saeed, ta bayyana haka yayin bikin miƙa wasu gine-gine da suka dace da kowane yanayi ga gwamnatin Jihar Jigawa, wanda aka gudanar a ƙauyen Chamo dake yankin ƙaramar hukumar Dutse, babban birnin jihar jigawa a ranar litinin da ta gabata.

Wafaa Saeed ta bayyana cewa UNICEF tare da haɗin gwiwar FCDO da sauran abokan hulɗa, ciki har da gwamnatocin Kano da Jigawa, sun ƙirƙiro shiri mai suna Climate Resilient Infrastructure for Basic Services (CRIBS) a fannin lafiya da Ilimi.

Unicef ta yaba wa Gwamna Umar Namadi bisa ci gaba da yaƙi da al’adar ba-haya a bainar jama’a, ta hanyar samar da isassun banɗakuna ga al’umma a birane da yankunan karkara .

Ta ce jajircewar UNICEF wajen rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a Jigawa, tare da ƙoƙarin gwamnatin Namadi a fannin ilimi, na nuna cewa matsalar za ta zama sai tarihi a nan gaba kaɗan.

Ita ma daraktan ayyuka ta ofishen cigaban ƙasashen waje na gwamnatin Birtaniya FCDO, Cynthia Rowe, ta bayyana cewa Najeriya na cikin ƙasashe masu fuskantar barazanar matsalolin sauyin yanayi.

A cewarta, Najeriya ce ta biyu a jerin ƙasashen da yara ke fuskantar matsala mafi girman haɗurran sauyin yanayi, wanda kai tsaye ke barazana ga rayuwarsu, girmansu, karatunsu da kuma cikar burinsu.

A jawabin sa, Gwamna Umar Namadi, ya yaba wa abokan hulɗarsu wato UNICEF wajen samar da ci gaba ga al’umma, inda ya bayyana irin wannan matakin a matsayin “dabarun da aka kirkira wajen yaƙi da sauyin yanayi.”

Namadi ya ce Jigawa na daga cikin jihohin da ke fuskantar bala’o’i kamar ambaliyar ruwa da fari, waɗanda ke shafar makarantu da cibiyoyin kiwon lafiya.

Gwamna Namadi ya yi alƙawarin ci gaba da tallafawa abokan hulɗar domin inganta walwalar yara, mata da jama’ar jihar baki ɗaya.

Wakilinmu na jihar jigawa ya rubuto cewa UNICEF tare da haɗin gwiwar Ofishin ci gaban ƙasashen waje na Gwamnatin Birtaniya (FCDO), sun miƙa gine-ginen da suka dace da yanayi ga gwamnatin jihar Jigawa, don rage tasirin sauyin yanayi a yankin da abin ya shafa

Gine-ginen da aka miƙa wa gwamnatin jihar sun haɗa da cibiyoyin kula da lafiya matakin farko da kuma makarantu na firamare da ke kauyan Chamo a ƙaramar hukumar Dutse.

By ukarofi