Dokar ta-ɓaci: Burin Tinubu ya cika a Ribas, inji kantoman jihar

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kantoman da Shugaba Bola Tinubu ya naɗa a Jihar Ribas a watannin baya, Ibok-Ete Ibas, ya ce umarnin shugaban ƙasar na a samar da lumana a harkokin siyasar jihar ya kammala.

Ibas ya bayyana haka ne a jiya Juma’a a Gidan Gwamnatin jihar da ke Fatakwal yayin gabatar wa tawagar Hukumar Zaɓen jihar (RSIEC) rahoton zaɓen ƙananan hukumomin da aka gudanar a kwanan nan.

Ya ce, umarnin na Shugaba Tinubu ya haɗa da dawo da bin doka da oda da walwalar al’ummar jihar, sake kafa cibiyoyin dimukraɗiyya da kuma warware matsalolin rikicin siyasa da aka ɗauki watanni ana fama da shi a jihar.

A ranar 18 ga watan Maris, 2025, Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a Ribas na tsawon wata shida tare da naɗa Ibas a matsayin kantoma sakamakon ƙamarin rikicin siyasa da ya kai ga majalisar dokokin jihar ta yi barazanar tsige Gwamna Siminalayi Fubara.

Akan haka ne Shugaban Ƙasar ya rushe zaɓaɓɓun ƴan siyasar jihar tun daga gwamna da ƴan tawagarsa har zuwa ƴan majalisar dokokin jihar.

By Babaji