
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Litinin Alƙalin Alƙalan Nijeriya, Kudirat Kekere-Ekun za ta rantsar da sababbin manyan lauyoyin Nijeriya, wato SAN guda 57.
Taron ɓangare ne na shirye-shiryen zagayowar zangon 2025/2026 na shekarar shari’a.
Ana sa ran gudanarwa a farfajiyar kotu ta Kotun Ƙoli, kamar yadda Daraktan Hulɗa da jama’a na Kotun Ƙoli, Festus Akande ya bayyana a Abuja cikin wata takarda.
Haka kuma ana tsammanin ganin manyan alƙalai a ɓangaren harkar shari’a su gabatar da jawabai musamman kan ababen da suka shafi matakin fannin nasu.
Kazalika, za a fara ne da misalin ƙarfe 10 na safe, inda ake sa ran halartar Antoni-Janar na ƙasa, Shugaban tawagar manyan lauyoyin Nijeriya (BOSAN) da Shugaban ƙungiyar lauyoyi (NBA) da dai sauransu.
