Gwamnatin Katsina za ta gyara makarantun firamare da suka lalace

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

A zaman majalisar zartarwa karo na 14 a wannan shekarar, gwamnati ta amince da gyara makarantun firamare da suka lalace a faɗin jihar. Za’a fara da guda 10 kowace ƙaramar hukuma 34 da ke jihar.

Kwamishinan yaɗa labarai Dr Salisu Bala Zango ya sanar da haka da yake wa manema labarai bayanin sakamakon taron majalisar zartaswa ta Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dikko Raɗɗa.

Ya bayyana cewa majalisar zartarwa ta kuma amince da ƙara sayen katan 5,000 na harsasai don cigaba da yaƙar yan ta’adda.

Haka kuma matasa da suka gama karatu ba su da aiki kuma suna sha’awar kasuwanci, kwamishinan ya ce gwamnati ta samar da tsarin bada bashi mara ruwa ƙarƙashin sabon shirin Graduate Entrepreneurship Empowerment Program a KASEDA.

Majilasar ta amince da gina tagwayen hanyoyin Daura Western Byepass a garin Daura mai tsawon kilomita 14.43 (14.43KM).

Gwamnatin Katsina ta amince ta sayo manyan motoci guda 30 masu cin mutun 40 ga hukumar KTSTA don sauƙaƙa zirga-zirga a Jihar Katsina.

Dr Bala Zango ya kuma sanar da cewa gwamnatin za ta tallafawa mata da suka rasa mazajensu a hare-haren yan ta’adda da kuma gajiyayyu a faɗin jihar.

By ukarofi