
Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON) ta sanar da kuɗin zuwa aikin Hajjin shekarar 2026 ga masu niyya tare da rage farashinsa daga yadda ta sanar a baya.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce an yi ragin N200,000 daga kuɗin hajjin domin sauƙaƙa wa alhazai daga Nijeriya damar aiwatar da ibadar cikin sauki da rangwame.
NAHCON ta bayyana cewa, hakan ya biyo bayan tattaunawa da hukumomin Saudiyya da nazari akan musayar kuɗaɗe da kuma ƙoƙarin gwamnati na tallafa wa alhazai.
Ta kuma buƙaci maniyyata da su cigaba da bin shawarwari da jaddawalin da aka tsara, tare da tabbatar da cewa sun bi dukkan matakan da ake buƙata wajen samun gurbin zuwa ƙasa mai tsarki domin ibadar.
Ana sa ran sauƙin kuɗin zai ƙarfafa gwiwar masu niyyar zuwa hajji da dama, musamman duba da yadda al’umma suke fuskantar ƙalubalen tattalin arziƙi.
Da fari NAHCON ta sanar da kafin alƙalami na miliyan N8.5, wanda a yanzu sakamakon ragin ya koma miliyan N8.31.
Saidai kuɗin zai iya bambanta bisa la’akari da jiha ko yankin da mutum yake inda kamar a yankin Maiduguri-Yola, ya kama N8.44m, sai kuma N8.76m ga ƴan jihohin kudu, amma a yanzu kowane ɓangare ya samu ragin N200,000.
