NIJERIYA A 65: Ƙalubalen shugabanni da matasa

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A ranar Laraba da ta gabata, ’yan Nijeriya suka gudanar da bikin murna da zagayowar Ranar Samun ‘Yancin Kan ƙasa daga turawan mulkin mallaka na ƙasar Ingila, wanda aka saba gabatarwa duk ranar ɗaya ga watan Oktoba. Babu shakka wannan babbar rana ce a tarihin Nijeriya, duba da irin ƙalubale da matsalolin da ƙasar ta daɗe tana gwagwarmayar tabbatar da su, tun daga 1960 shekarar da aka samu ’yancin kai.

A kowace shekara, ranar samun ‘yancin kai tana kasancewa rana ce mai muhimmanci sosai, domin tana tunatar da mu game da tarihi, jaruman da suka yi gwagwarmaya don tabbatar da ɗiyaucin ƙasar nan, da kuma alƙawarin da aka ɗauka na gina ƙasa mai inganci, tausayawa, da samar da adalci ga kowa.

Bikin ranar samun ‘yanci dama ce da al’ ummar ƙasar nan za su zurfafa tunani da sabunta kishin ƙasa, da sake jaddada alƙawarin zama ’yan ƙasa nagari. Duk da ƙalubalen da Nijeriya ke fuskanta a halin yanzu kamar yadda Gwamnatin Tarayya ta sanar da dakatar da manyan shagulgulan faretin bikin a wannan shekara, wannan rana tana ƙarfafa mana gwiwa ga yin nazari da kuma aiki tuƙuru wajen ganin ci gaban ƙasar nan ya inganta, kuma ya ɗore. 

Taken bikin cika shekaru 65 da samun ’yancin kan Nijeriya na bana da ke nuni ga buƙatar dukkan ’yan Nijeriya mu haɗa kai domin samar da ingantacciyar ƙasa, ya koyar da mu cewa, aikin gina ƙasa ba na gwamnati kaɗai ba ne, aikin kowa ne. Kuma kowanne ɗan ƙasa abokin kowa ne, ba tare da nuna wariya ko bambanci ba.

Sanin kan mu ne, Nijeriya na fuskantar manyan matsaloli da suka haɗa da rashin ingantaccen tsaro, talauci, hauhawar farashin kayayyaki, da kuma rashin ingantattun hanyoyin sufuri da wutar lantarki. Waɗannan matsaloli da suka yi wa ’yan Nijeriya dabaibayi su ne suka sanya ‘yan Nijeriya ke ji kamar ba su kai inda aka yi alƙawarin kai wa ba bayan shekaru 65. Wasu kuma na ganin babu wata hujja ta yin biki, saboda hankalin ’yan Nijeriya ba a kwance yake ba. Ko a jawabin da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar ta kafafen watsa labarai, ya bayyana cewa kodayake matsalolin mu sun yi yawa, gwamnati na aiki tuƙuru wajen shawo kansu domin mayar da ƙasa cikin kwanciyar hankali da ci gaba.

Shekaru 65 bayan samun ’yancin kai, manyan ƙalubalen da ke gaban shugabannin ƙasar nan ya haɗa da samar da ingantaccen tsaro da zaman lafiya mai ɗorewa, musamman a yankunan Arewa maso Gabas da ke fama da hare-haren ‘yan ta’adda. Taƙaita matsalolin tattalin arziƙi, domin rage raɗaɗin talauci ga talakawa. Da inganta samar da ababen more rayuwa kamar su hanyoyi, wutar lantarki da ilimi. Sannan uwa-uba, haɓɓaka haɗin kai tsakanin al’ummomi daban-daban, domin tabbatar da gina ƙasa mai mutunta haƙƙoƙin kowa da yi wa kowa adalci. Da jawo hankalin matasa da bada damar zama manyan gobe, ta hanyar ba su tallafin ilimi, ƙarfafa musu gwiwa don su bayyana ƙwarewa su da basirar su, da kuma samar musu da tallafin sana’o’i da ayyukan yi.

Manufar wannan rana ba kawai tunawa da ‘yancin kai ba ce, har’ilayau, dama ce ta mayar da hankali kan abubuwan da za su dawo da yardar talakawa kan shugabannin su, sabunta kishin ƙasa da ƙarfafa haɗin kai tsakanin ‘yan ƙasa da shugabanni domin ganin Nijeriya ta cimma burinta ta na zama ƙaƙƙarfar ƙasa abin misali ga kowacce ƙasa ta duniya.

Yana da muhimmanci ga matasan ƙasar nan su fahimci cewa su ne manyan goben da, ake sa ran su ne za su kawo canjin da zai gyara ƙasar nan. Sannan hakkin su ne su ɗauki nauyin jan ragamar jagorancin ƙasar nan, domin tabbatar da ganin an kai ga cimma hadafin cigaba aka gina Nijeriya a kai. Yana kyau matasa mu yi amfani da damar da muke da ita wajen yin tasiri a cikin al’umma ta hanyar shiga harkokin siyasa, gudanarwa, da samar da mafita ga matsalolin da ƙasa ke fuskanta.

Babu shakka a lokaci irin wannan matasa na da damar da za su bayyana muradun su da kuma ƙƙarfafa haɗin kai a tsakanin su, domin samun cigaba mai ɗorewa, tare da yin kira ga shugabannin ƙasa da su ba su damar shiga a dama da su wajen tsara makomar ƙasa. Wannan yana ƙara jawo hankalin matasa kan muhimmancin shiga cikin tsarin dimokuraɗiyya da kuma aikin ci gaban ƙasa.

Lallai ne mu tabbatar mun taimaka wajen ajiye bambance-bambancen siyasa, addini da ƙabilanci, don haɗin kan ƙasar mu ya inganta. Kuma shugabanni su ɓullo da muhimman tsare-tsaren farfaɗo da tattalin arziƙi ta hanyar sauƙaƙa haraji da bunƙasa masana’antu, jawo hankalin ’yan ƙasashen waje don zuba jari a ɓangarori daban-daban, ba tare da an yi kashe mu raba, ko an ci amanar ’yan ƙasa ba. 

Ubangiji Allah Ya ba mu zaman lafiya, ci gaban ƙasa, zaman lafiya da ingantaccen tsaro, da zai sa mu samu damar gina gagarumar ƙasa da kowanne ɗan Nijeriya zai yi alfahari da ita. Zan rufe da kalamin shugaban ƙasa Bola Tinubu da ke cewa, mu guji raina ƙasar mu da faɗar maganganu na rashin kishi ga shugabannin mu! 

Barkan mu da cika shekaru 65 da samun ’yancin kan Nijeriya!

By ukarofi