Addini, Abduljabbar da Triumph

Spread the love

Daga TY TEBO

Bangaren su Triumph suna fara taksisin nassi ne kafin su inganta. Daga ya inganta ya zama wahayi kuma dole kowa ya karbe shi. Bangaren su Abduljabbar kuma suna fara nemo hikimar ne kafin su yarda ya inganta. Su falsafa suke fara fifitawa.

ɓangare na farko suna koyo ƙur’ani da tafsiri ne sai su gane ingancin hadisai, anan ne suke gane alakar ayoyi da rayuwar manzon Allah (s.a.w). Bangare na biyu kuwa saboda sun gina addininsu ne kan soyayyar ma’aiki, sai suka dauki ƙur’ani da tarihin manzon Allah (s.a.w), a nan ne suka samu sha’awar al’adun Larabawa har suke kara shiga fagen Larabci.

Ana samun malaman hadisi daga bangaren su Triumph saboda fifita ƙur’ani, su kuma bangaren su Abduljabbar ana samun masana Fiƙhu saboda sun fifita Larabci. Wannan ya sa idan aka zo falsafa da kasidu sai Sufaye su yi fincinkau, amma idan aka zo fagen addini sai yan Salafiyya su yi ta raddi da ayoyi da hadisai.

’Yan Faira suna amfani da wakoki ne da falsasa shi ya sa ba su san Tauhidi ba. Suna amfani ne da hankali shi ya sa suke ganin komai ma Allah ne. Karshe sai a samu wadanda ba sa salla, daga karshe ma su haukace ko su daina addinin. A daya gefen kuma ake samun masu ganin duk wanda ya karyata nassi ya kafirta, kashe shi za ayi tun da ya karyata Allah ya bar addini.

Masu da’awar “orientalism” suna ganin dole ne addini ya zama “liberal”, wanda kuma hakan ya sabawa yan “Islamic Thought and Ciɓilization” da ke aiki dan gano falsafa, kimiyya da fasahar addini da cigaba. Wasu na ganin da siyaki (conteɗt) kadai za ayi aiki sai nassi ya tafi da zamani, bayan kuma zamani ne ya samu nassi. 

Akwai masu ganin abin da ya faru a zamanin annabi (s.a.w) bai kamata ayi aiki da shi a yau ba. Anan wajen aka samu bijirowar matsaloli da suka shafi “asbabun nuzul” har wasu ke tafiya kan mas’alar “nasik wal mansuk”. Wasu ma na ganin duk ayar da aka soke hukuncinta ta tafi kenan. Wasu kuma suka ce dole ne a karbe ta tun da ta zama wahayi. 

Masu fifita nassi da fassarar magabata na kwarai (Sahabbai da dalibansu) su ne ke tafiya kan abin da annabi ya bari na ilimi. Su waye ne a yau? Su kuma wadanda suka ware wasu sahabbai a gefe bayan mutuwar annabi sai suke zarginsu da zagon kasa da ganin ko da wani sahabi ya ruwaito hadisi cikinsu ba shi da inganci. Ina adalci a nan? 

Yan boko a Arewa da wadanda ba su gama fahimtar addini ba suna cikin rudani saboda kan masu addini a rabe yake, an cusa siyasa, gaba da munafurci. Yanzu wasu na ganin Abduljabbar a matsayin mai kishin addini, amma a hakika mabarnaci ne da ya yi sakaci har ya shiga masifar da ya shiga. Taurin kai, izza, da tsoron rasa mabiya ya jefa shi cikin zafi har ta kai yana share gumi tare da kurbar ruwa da hannun hagu. 

Da Abduljabbar da Triumph duk kore da’ifanci suke. Titsiyen da aka yi wa Abduljabbar ya kamata a yi wa Triumph, sai dai kuma akwai wani haske da ya bayyana; Abdujabbar korewa yake tare da kirkiro fassarar ganin dama yana laftawa kan annabi (s.a.w) dan a tsani marawaitan hadisan saboda kiyayyarsa ga Izala/Wahabiyawa. 

Ba za a ce Triumph ya tabbatar da fassarar da ya yi ba kan annabi ba, kuma a iya saurarona ban ji inda ya siffanta annabi (s.a.w) da tumaki ba. Na dai ji ya haska cewa irin wannan karamar karyar da ake jinginawa annabi ba za ta kara masa komai ba, yana da abin da ba sai an masa karya ba za a nuna darajarsa; idan kuwa wannan ne ai tumaki ma akan same su da shi. Kenan hadisi bai inganta ba. 

Tun da ya ce bai inganta ba ya zo shi ya rusa. Kuma a tambaye shi ya yi karin haske kan misalinsa dan kare martabar annabi tun da ya kawo shakku. Masu ikirarin inganci kuma su kare hadisinsu ta hanyar rusa da’awar Triumph maras tushe. Idan ya inganta a tambaye shi ya yarda, idan ya yarda anyi nasara a da’awa kuma an taimake shi. Idan bai inganta ba gaskiya tayi halinta. 

Daga karshe mu da mu ka yarda addini an gina shi kan wasadiyya ne, hadin kai, zaman lafiya da kira zuwa a bautawa Allah (koyi da kyakkyawa da hani da mummuna a aikace), muna cewa yan Arewa su rike AI, karatun boko, takanologi, IT, ilimin tattalin ariki, sanin yanci a kundin tsarin mulki, bin doka a Nigeria da kuma kira a gwamnati tayi adalci. Malamai su daina ci da addini, tunzura mabiya, kuma iyaye su daina haihuwa barkatai suna watsar da yayansu a titi karshe suna zama yan faira, BH, yan daba, kwacen waya, da yan ta’addan daji.

Ty Tebo ma’abocin shafukan sada zumunta ne a Nijeriya

By ukarofi