
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jam’iyyar adawa ta ADC ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta fayyace haƙiƙanin abinda ke faruwa akan rahotannin da ke yawo cewa an yi yunƙurin juyin mulki ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Ta yi gargaɗin kada a riƙa amfani da jita-jita wajen rufe bakin ƴan adawa ko kuma karkatar da tunanin al’umma game da gazawar gwamnati.
A wata takarda daga Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar, Bolaji Abdullahi a ranar Litinin, jam’iyyar ta ƙalubalanci Shugaba Bola Tinubu akan kada ya yi amfani da zargin juyin mulki wajen rufe bakin ƴan adawa ko jagororinsu da sunan tsaron ƙasa.
Ta ce, duk wani yunƙuri na siyasantar da al’amarin da fakewa da sunan hakan wajen cigaba da danniya ga al’umma, zai zama barazana ga harkar dimukraɗiyyar Nijeriya da ƴancin al’umma.
Hakan na zuwa ne a lokacin da gidajen jaridu ke ruwaito cewa Sashen Leƙen Asiri (DIA) na Hedikwatar Tsaro ya kama wasu manyan jami’an sojoji da hannu a kitsa juyin mulki da kifar da gwamnatin Shugaba Tinubu.
Tuni Hedikwatar ta ƙaryata rahotannin da cewa ƙirƙirar su aka yi da nufin ruɗar da al’umma.
Saidai duk da haka, ADC ta tirje akan cewa gwamnatin ta yi haka ne domin ta ruɗar da tunanin al’umma a Nijeriya, domin a cewarta, har yanzu hakan bai wadatar ba na gamsar da al’umma akan al’amarin.
