Shugaban matasa ya canja sheƙa daga APC zuwa ADC a Kebbi 

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi 

Wani ɗan kasuwa mazaunin birnin Legas kuma shugaban matasa a mazaɓar Sauwa/Kaurar Sani a ƙaramar hukumar Argungu Alhaji Zaki Dalatu ya canja sheƙa daga Jam’iyyar APC zuwa ADC.

Da ya ke zantawa da manema labarai a garin Argungu yayin wata ziyara da tawagar sa ta kai wa Honarabul Sani Yakubu (Yar Giwa) Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Argungu da Augie.

Alhaji Zaki ya bayyana cewa ya baro kasuwancinsa da ya ke yi a Legas saboda kawai ya jaddada barin Jam’iyyar APC mai mulki zuwa Jam’iyyar ADC ta adawa tare da dukkan magoya bayansa.

Ya ƙara da cewa akwai matasa sama da hamsin da ke kasuwanci a ƙarƙashin sa daga nan gida da kuma Legas kuma ya umarce su da duk wanda ya san katin zaben sa ta bata ko ta lalacce da ya dawo gida ya karbi wata, haka-zalika matasa waɗanda suka kai shekaru goma sha takwas su je su karɓi sabon katin jefa ƙuri’a.

Ya ƙara da cewa an sha amfani da su amma ana mayarda su shanuwar aare bayan an ci zabe saboda haka yanzu su ma za su canja sheƙa su koma inda suke ganin ba za a manta da yankin su ba.

Alhaji Zaki ya bayyana cewa duk wanda ke garin Dalatu, Kaurar Sani, Bangola, Tungar Rairai har zuwa garin Sauwa ya san irin abinda ya ke yi amma daga cikin yaran sa ba wanda ya ci moriyar wani aiki daga wannan gwamnatin tun kama daga tarayya zuwa jiha ballantana ƙaramar hukumar mulki.

By ukarofi