Su wane ne sababbin shugabannin rundunonin sojan Nijeriya?

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Nijeriya ta shiga sabon babi a tsarin tsaron ƙasa bayan naɗa sababbin manyan hafsoshin rundunonin soji da suka fito daga sahun gogaggun jami’ai masu ƙwarewa a fannin yaƙi, ilimi da jagoranci. Sabbin hafsoshin – waɗanda suka haɗa da manyan kwamandoji daga rundunar sojojin ƙasa, sama da na ruwa – na daga cikin manyan jami’an da suka fi ƙwarewa da samun horo a cikin gida da ƙasashen wajen Nijeriya.

Waɗannan manyan hafsoshin sun shafe shekaru da dama a filin daga, aikin tsaro da jagorantar rundunoni a Nijeriya da ma ƙasashen Afirka, inda suka taka muhimmiyar rawa a yaƙin da ake yi da ta’addanci da ƙarfafa tsarin tsaro na ƙasa.

Babban Hafsan Tsaron ƙasa – Laftanar Janar Olufemi Olatubosun Oluyede:

An haifi Laftanar Janar Oluyede a ranar 21 ga Yuni, 1968, a Ikere-Ekiti. Jagora ne mai zurfin ilimi da gogewa a yaƙin da ta’addanci da kuma ayyukan haɗin gwiwar tsaro tsakanin rundunoni.

Ya fara aiki a matsayin hafsan sojin ƙƙsa kafin ya zama Babban Hafsan Soji (COAS) a 2024, sannan daga baya aka ɗaga shi zuwa Babban Hafsan Tsaro (CDS).

Salon jagorancinsa ya ta’allaƙa ne da ƙarfafa kwarin gwiwar sojoji, gyaran tsarin runduna, da haɓaka haɗin kai tsakanin jami’an tsaro.

Babban Hafsan Sojojin ƙasa – Manjo Janar Waidi Shaibu:

An haifi Manjo Janar Waidi Shaibu a ranar 18 ga Disamba, 1971, a ƙaramar Hukumar Olamaboro ta Jihar Kogi. Ya shiga makarantar soja ta Nijeriya (NDA) a shekarar 1989 a matsayin ɗan ajin 41 kuma aka ɗora masa muƙamin Laftanar na biyu a shekarar 1994 a rundunar sojojin bindigogi masu sulke (Armour Corps).

Janar Shaibu yana daga cikin jami’an da suka fi zurfin ilimi a sojojin ƙasa. Ya samu digiri a fannin Injiniya daga NDA Kaduna, sannan ya yi karatun digiri na biyu a fannin Gudanar da Harkokin Jama’a (Jami’ar Kalaba), da karatun dabarun tsaro da dabarun jagoranci daga jami’o’in Ibadan da National Defence University, Washington D.C., Amurka. Haka kuma ya halarci horo a Harvard Kennedy School da cibiyoyin soja a Ghana, Kenya da Nijeriya.

A filin daga, ya taka rawa a Operation Zaman Lafiya, Lafiya Dole, Tura Takaibango, Haɗin Kai, da kuma ayyukan wanzar da zaman lafiya na Majalisar ɗinkin Duniya a Sudan da Liberia. Ya riƙe muƙamai da dama, ciki har da kwamandan 21 Armoured Brigade Bama, kwamandan runduna ta 7 (Division 7), kuma kafin yanzu shi ne Daraktan Bincike da Ci gaban Makamai a cibiyar Heritage and Future Centre.

An karrama shi da lambobin girmamawa ta ‘Distinguished Service Star’ (DSS), Field Command Medal (FCM), da Purple Heart Medal saboda bajintarsa a yaƙin da ta’addanci.

Babban Hafsan Sojojin Ruwa – Rear Admiral Idi Abbas:

Rear Admiral Idi Abbas, ɗan asalin Jihar Kano, an haife shi a ranar 20 ga Satumba, 1969. Ya shiga NDA a ajin 40 kuma ya zama jami’i a shekarar 1992.

Ya yi aiki a wurare daban-daban, ciki har da Flag Officer Commanding Central Naval Command, Bayelsa, inda ya samu nasara wajen rage ayyukan fashi a teku da satar mai. Yana daga cikin jami’an da ke taka muhimmiyar rawa wajen tsare-tsaren haɗin gwiwar tsaro a Nigerian Army Heritage and Future Centre.

Rear Admiral Abbas mutum ne mai nutsuwa da ƙwarewa a tsare-tsaren dabarun yaƙi, kuma yana da aure da ‘ya’ya.

Babban Hafsan Sojojin Sama – Air Vice Marshal Sunday Kelvin Aneke:

An haifi AVM Aneke a ranar 20 ga Fabrairu, 1972, a Makurdi, Jihar Benuwe, daga asalin ƙaramar hukumar Udi ta Jihar Enugu. Ya shiga NDA a ajin 40 kuma ya zama jami’i a rundunar sojin sama a 1993.

Yana da digiri a Physics, digiri na biyu a Diplomacy, da kuma karatu a Aviation Safety Management daga jami’ar Embry-Riddle University a Amurka. Haka kuma ya halarci US Air War College.

A fagen tashi da jiragen soja, yana da fiye da awanni 4,300 na tashi a jiragen Gulfstream V, Falcon 900, Hawker 4000 da sauransu. Ya taɓa zama kwamandan 307 Eɗecutive Airlift Group, sannan mataimakin kwamandan Nigerian Defence Academy.

Babban Hafsan Leƙen Asirin Soja – Manjo Janar Emmanuel Akomaye Undiandeye:

An haife shi a Bedia, ƙaramar hukumar Obudu ta Jihar Kuros Ribas, a ranar 2 ga Satumba, 1968. Ya yi karatu a NDA Kaduna da Royal Military Academy Sandhurst a Birtaniya.

Ya taka rawa a ayyukan zaman lafiya na Majalisar ɗinkin Duniya a Liberia da Abyei, kuma ƙwararre ne a fannin bincike da tsare-tsaren leƙen asiri. Yana memba na National Defence University (Washington DC) da Nigerian Army Resource Centre.

Kammalawa:

Sababbin hafsoshin sun fito daga sahun jami’an da suka fi samun horo a duniya, tare da gogewa a yaƙin da ta’addanci, ayyukan wanzar da zaman lafiya, da dabarun tsare-tsare na tsaro.

Naɗinsu yana nuna sabon salo na gyaran tsaro, haɗa kai tsakanin rundunoni, da ƙarfafa nagartar aikin soja a Nujeriya, wanda ake sa ran zai taimaka wajen tsare rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasa.

By ukarofi