Wata ƙungiya ta nemi Bello Matawalle ya sake tsaya wa takarar kujerar Gwamnan Zamfara

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban ƙungiyar Yarima Tsiga Solidarity Forum Alhaji Farouk Ibrahim Tsiga yayi wannan kira a Katsina.

Ya bayyana cewa tsohon gwamnan wanda a yanzu yana riƙe da muƙamin ƙaramin ministan tsaro yayi abin a zo a gani a lokacin da yake Gwamnan Zamfara.

Tsiga wanda babban aminin ministan ne ya ce lokacin Bello Matawalle ya na gwamnan Zamfara ya tabbatar da jajircewa da ƙwarewa wajen shugabantar jihar.

“An sami cigaba a gwamnatin Matawalle ta fannin kiwon lafiya, Ilimi,noma da bunƙasa rayuwar al’ummar jihar musamman mata da matasa,”inji Farouk Tsiga.

Dr Bello Matawalle ya yi aikace-aikace na bunƙasa tattalin arzikin Jihar Zamfara da suka haɗa da gyaran manyan asibitoci da gina guda 147 a cewar shugaban ƙungiyar.

Haka kuma ministan ya sanar da motocin ɗauka marasa lafiya guda 21 da Bubura na hawa masu ƙafa uku suma na ɗaukar marasa lafiya guda 147 da kakkafa na’urorin kiwon lafiya a manyan asibitoci na jihar Zamfara, Tsiga ya bayyana haka.

Shugaban ƙungiyar yana mai imanin cewa Bello Matawalle ya na da damar magance matsalar tsaro da ta addabi jihar duba da ƙwarewa a matsayin sa na mai riƙe da muƙamin ƙaramin ministan tsaro.

Ya ce ƙungiyar su za ta cigaba da faɗakar da al’ummar Jihar Zamfara kan muhimmancin sake dawo da Bello Matawalle a matsayin gwamnan jihar Zamfara a karo na biyu domin ya cigaba a inda ya tsaya.

Tsiga yayi kira ga tsaffin gwamnonin jihar waɗanda dukkan su ya’yan jam’iyyar APC ce,Jakada Yuguda da shugaban jam’iyyar APC a jihar Alhaji Yusuf Idris da sauran masu ruwa da tsaki na kimiyya a jihar da su nemi ministan ya dawo ya sake tsayawa takarar kujerar Gwamnan jihar.

By ukarofi