MURIC ta buƙaci Tinubu ya sauke Amupitan daga shugabancin INEC

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

ƙungiyar Kare Muradun Musulmai (MURIC) ta buƙaci a gaggauta tsige Farfesa Joash Amupitan daga shugabancin Hukumar Zaɓe ta ƙasa (INEC), saboda matsayinsa kan batun rashin tsaro a Nijeriya.

Manhaja ta rawaito cewa, a cikin wani rubutu a baya, Amupitan wanda a lokacin malami ne a Jami’ar Jos da ke Jihar Filato, ya ce “abu ne sananne cewa ana aikata laifuka a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa a Nijeriya, musamman laifukan da suka shafi cin zarafin bil’adama, laifukan yaƙi da kuma kisan ƙare dangi.”

Ya ƙara da cewa: “Kalma guda da hukumomin Nijeriya da masu bincike na ƙasa da ƙasa da masu bayar da rahoto ba su ambata ba (ko kuma suka ki ambata) dangane da dogon rikicin da ake fama da shi a Nijeriya ita ce ‘kisan ƙare dangi.’ Shin wannan mantuwa ce ta gangan ko kuskure ne?

“Zargin shiga tsakanin gwamnati da kungiyoyin da ba na gwamnati ba wajen aikata laifukan ƙasa da ƙasa a Nijeriya ya ƙara dagula lamarin da tuni ya yi tsauri.

“ƙungiyar Boko Haram tana da burin sauya Nijeriya zuwa tsarin Musulunci. ’Yan bindigar ƙabilar Fulani, a nasu ɓangaren, sun shiga irin wannan rikicin na adawa da Kiristoci kamar yadda Boko Haram ke yi,” kamar yadda ya rubuta a lokacin.

Haka kuma ya kira Kwamitin Tsaro na Majalisar ɗinkin Duniya, hukumomin majalisar da manyan ƙasashen duniya da su shawarci ƙasashen da suka rattaɓa hannu kan yarjejeniyar kisan ƙare dangi su kai Nijeriya kotun kasa da kasa (ICJ) saboda gazawar ta wajen hana da hukunta kisan ƙare dangi kamar yadda aka tanada a cikin saɗarori na 8 da 9 na yarjejeniyar; sannan su yi la’akari da shigar dakarun Majalisar ɗinkin Duniya, ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) ko na ECOWAS a matsayin mataki na ƙarshe, bisa ga saɗara ta 42 a Kundin Majalisar ɗinkin Duniya.

To sai dai a cikin wata sanarwa da shugabanta, Farfesa Ishaƙ Akintola ya fitar, MURIC ta gargaɗi cewa duk wanda ya shafi irin wannan rubutu mai cike da cece-kuce ba za a iya amincewa da shi wajen jagorantar harkokin zaɓe ba a Nijeriya.

“Mutumin da ya rubuta wasiƙar ƙiyayya ga Shugaba Donald Trump kan Musulmai a Arewacin Nijeriya ba za a iya tsammanin adalci daga gare shi wajen gudanar da zaɓe a Nijeriya ba,” inji shi.

MURIC ta ce rawar da ake zargin shugaban INEC ya taka a cikin rahoton ta lalata amincewar da jama’a suka yi masa a baya kuma tana haifar da “barazana ga Musulmai ’yan takara a Arewa ta Tsakiya da sauran sassan kasar.”

“Tun daga lokacin da wannan bayani ya fito, Amupitan ya zama wanda Musulmai ba sa son ganin ya taka rawa a harkokin zaɓe. Muna bayyana cikakkiyar rashin amincewa da shi a matsayin shugaban INEC,” inji ƙungiyar.

ƙungiyar ta kuma buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya tsige shugaban INEC daga muƙaminsa tare da naɗa wanda zai samu karɓuwa a faɗin ƙasa.

“Muna ba da shawarar cewa a zabi wani wanda ya cancanta, da zai samu karbuwa a faɗin ƙasa, wanda zai fi dacewa ya kasance mai addini ɗaya da Amupitan amma daga wani yanki daban na siyasa,” inji Akintola.

By ukarofi