
Shugaban Karamar Hukumar Bichi, Alhaji Hamza Sule Mai Fata, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da shirin bai wa mata jari a sakatariyar ƙaramar hukumar.
Manufar shirin dai ita ce, taimaka wa mata marasa karfi akan don tsayawa bisa gwadaben neman na kansu ta hanyar rage barace-barace a cikin al’umma da kuma bunƙasa tattalin arziƙinsu.
Shugaban Karamar Hukumar Bichi, Alhaji Hamza Sule Mai Fata tare da mata kimanin dari da suka amfana da jarin dubu hamsin-hamsin a yankin, sun gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa kokarinsa na hidimtawa al’umar Kano ta kowane fanni.
“Mun gode, an ba mu kudi hannu da hannu, Allah ya saka da alheri.” Amina Musa Mazabar Saye.
“Saka su zan yi a sana’a. Ina yi wa Gwamna godiya, Allah maimaita gwamnatin nan tamu.” Sa’ade Idi Wajila, Mazabar Fagolo.
Taron ƙaddamar da shirin, ya samu halartar shugaban yankin, Alhaji Hamza Sule Mai Fata, Sakataren Mulki, Hon. Anas Muhammad Abdullahi, Daraktan Mulki, Alhaji Abba Muhammad Diso, Shugaban Kwamitin CRC, BC Bello Gambo Danzabuwa, kansiloli, shugabannin sassa da kuma sauran ma’aikata na karamar hukumar.



