
Gwamnatin Tarayya ta musanta rahotonnin da ake yaɗawa cewa ta umarci a rufe makarantu a faɗin ƙasar daga ranar Litinin mai zuwa.
A wata sanarwa da Ma’aikatar Ilimi ta fitar, ta ce rahoton ba gaskiya ba ne.
“Rahoton ba daga gwamnatin tarayya yake ba, ko ma’aikatar ilimi, ko wata ma’aikatar ilimi ta jiha, ko wata hukumar tsaro.”
A ranar Juma’a gwamnati ta sanar da rufe makarantun sakandare na kwana su guda 41 mallakarta da ake kira da Unity Schools a faɗin ƙasar.
Wannan umarni na zuwa ne bayan sace ɗalibai mata 25 a jihar Kebbi da kuma wasu 315 a jihar Neja a ranakun Litinin da kuma Juma’ar nan.
