
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Al’umma ta cigaba soka game da rashin halartar gwamnonin arewa taron bikin cikar Ƙungiyar Mashawartan Arewa (ACF) shekaru 25 da kafuwa, wanda aka gudanar a Kaduna, ranar Asabar.
Hakan ya sa Ƙungiyar Gwamnonin Arewa (NGF) ta fitar da saƙon ƙarin haske akan hukuncin duba da yadda wasu ke yi wa matakin kallon abinda bai dace ba.
Bikin ya samu halartar manyan baƙi daga ciki da wajen arewa, tun daga ranar farko har zuwa ranar rufewa, waɗanda su ka haɗa da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Alhaji Atiku Abubakar, hamshakin attajirin Afirka Aliko Ɗangote, Abdulsamad Isiyaka Rabiu (BUA), Mai Alfarma Sarkin Musulmi Dr. Muhammad Sa’ad Abubakar na III, Sarkin Ife, Sarakunan Dutse, Zuru, Fika, da Biu.
Akwai kuma gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi, mataimakan gwamnonin Kaduna, Gombe da kuma Yobe waɗanda su ka wakilci gwamnoninsu. Sannan akwai duka tsoffin gwamnonin jihar Kaduna tun daga 1999 zuwa 2023, tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamiɗo, na Sokoto Aliyu Magatakarda Wamakko, wakilin Abdulaziz Yari Abubakar, da dai sauransu.
Kakakin Majalisar Wakilai Tajuddeen Abbas shi ne ya wakilci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Barau Jibrin kuma ya wakilci Shugaban Majalisar Godswill Akpabio, yayin da tsohon gwamnan jihar Kebbi kuma Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziƙi Sanata Atiku Bagudu kuma ya wakilci Ministoci.
Babban abin da aka fi tatatunawa a taron shi ne lamarin matsalar tsaro da Arewa ke fuskanta a yanzu, inda manyan masu jawabi irin tsohon shugaban ƙasa Yakubu Gawon wanda ya tura wakili, da kuma tsohon Babban Hafsan Sojin Ƙasa Janar Tukur Yusuf Buratai da Sarkin Musulmi da Sarkin Ife da tsohon ɗan takaran shugaban ƙasa na SDP Adewale Adebayo da sauransu sun yi magana kan haɗin kan Najeriya da kuma samar da tsaro a Arewa, inda su ka yi ƙira ga mahukunta da masu ruwa da tsaki da a yi duk mai yiwuwa wurin dawo da zaman lafiya da aka san Arewa da Nijeriya ke da shi a baya tare da sake fasalin yanki domin inganta ta.
A ƙarshen taron an buɗe gidauniyar neman tallafin Naira biliyan 100 domin aiwatar da wani muhimmin aiki da ƙungiyar ACF ta ɗauko, inda a nan take,Ɗangote da BUA su ka bada Naira biliyan 5 (kowanensu biliyan 2.5).
Daga cikin waɗanda su ka sanar da bada tasu gudumawa akwai:
T.Y. Danjuma – Naira biliyan 1, Alhaji Dahiru Mangal – biliyan 1, A.A. Rano – miliyan 100, Majalisar Dattijai- miliyan 100, Abdul’aziz Yari Abubakar – miliyan 500, Turakin Gumel – miliyan 500, Senator Barau I. Jibrin – miliyan 50, Majalisar Wakilai – miliyan 100, Rotimi Amaechi – miliyan 30, Gwamnan Jigawa- Miliyan 50, Arewa Consultative BOT – miliyan 100, Nasiru Dano – miliyan 50, Sanata Alu Wammako da abokan Abdulaziz Yari su huɗu- miliyan 500, da dai sauransu.
Da yake jawabi ta bakin Daraktan yaɗa labaransa, Ismaila Uba Misilli, Shugaban NGF kuma Gwamnan jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ya ce rashin zuwan gwamnoni taron ba sakaci ko halim ko’in kula ba ne.
A cewarsa, hakan ya faru ne sakamakon da dama daga cikin su sun je ziyarar aiki ne a Birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu domin halartar taron G20, inda ake tattaunawa muhimman batutuwan da suka shafi harkokin tattali musamman na arewacin Nijeriya.
