Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace ’yan ƙasar Chana biyu da ke aiki a Jihar Kwara, a wani sabon hari da ya ƙara tada hankula a yankin.
Rahoton ya bayyana ne ta kafar SaharaReporters, inda majiyoyi suka tabbatar da cewa mutanen biyun ma’aikata ne a wani aikin gina hanya na kamfanin BUA a jihar.
An ce an sace su ne yayin da suke bakin aiki a kan aikin titin Bode Sa’adu–Kaiama–Kosubosu, inda ’yan bindigar suka mamaye wajen da daddare suka kwashe su zuwa wani wuri da ba a sani ba.
Wani jami’in tsaro ya ce harin ya faru ne a daren ranar 1 ga Disamba, 2025, tsakanin ƙarfe 11 na dare zuwa 4 na asuba.
A cewarsa, ’yan bindigar sun kai farmaki wajen aikin da ke ƙasa da kilomita biyu daga ƙauyen Bielesin/Fallah, kuma kusa da wani ƙauye mai suna Olokiti.
“Sun riƙa harbe-harbe na kimanin sa’o’i biyu zuwa uku kafin su yi garkuwa da ’yan ƙasar Chana biyu da ke aiki tare da kamfanin. Ya zuwa yanzu ba mu samu wata buƙata ko saƙon neman kuɗin fansa daga gare su ba, kuma babu asarar rai da aka samu sai dai sace waɗannan ma’aikata biyu,” inji majiyar.
Wannan hari na zuwa ne a daidai lokacin da rahotannin sace-sace ke ƙaruwa a sassan jihar.
A safiyar wannan rana, an kuma bayar da rahoton sace manoma shida a unguwar Lata da ke ƙaramar hukumar Patigi..
Rahoton ya ce, ’yan bindiga sun mamaye gonakin da sanyin safiya yayin da manoman ke aiki, suka tilasta musu shiga daji, kuma har zuwa yanzu babu wani sahihin bayani kan inda suke.
Wani mazaunin yankin ya kuma bayyana cewa a ranar Talata da ta gabata, an kori wasu ma’aikatan gona daga kan aiki, tare da kwace babur mai wata bakwai mallakin wani ɗan kasuwa na yankin.
ƙaruwar wazannan hare-hare na ƙara jefa jama’a cikin fargaba a yankunan Kwara ta Kudu da Kwara ta Arewa, inda mazauna ke cewa ’yan ta’adda na ƙara samun ƙarfin yin ta’asa ba tare da tarnaƙi ba.
