BIDIYO: Yadda Shettima ya isa wajen taron inganta al’umma daga tushe da aka yi a Akwa-Ibom

Spread the love

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya isa Cibiyar Inganta Al’umma ta Unyima Idem da ke mazaɓar Ukanafun/Oruk Anam a jihar domin bada caki ga mutane guda 1,000 da suak amfana da shirin Renewed Hope Initiative na Naira biliyan 1 da aka ware don tallafa wa magidanta

Shettima, wanda ya wakilci Shugaba Bola Tinubu a taron ya samu tarba daga manyan jami’an gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Maitaimakin Gwamnan jihar, Sanata Akon Eyakenyi.

An gudanar da taron ne da nufin tallafa wa magidanta guda 1,000 inda ake sa ran kowannensu zai samu jarin da zai faɗaɗa ko fara kasuwancinsa.

By ukarofi