Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ayyukan da shugaban ƙaramar hukumar Hon Ishaq Miƙidad AD Saudi ya aiwatar sun haɗa da gina sabuwar majalisar kansiloli ta ƙaramar hukumar Katsina da gina asibiti a Unguwar Yari Dake.
Akwai samar da cibiyar sadarwa ta ICT domin inganta koyon zamani da gudanar da ayyukan gwamnati da sayen motoci ga wasu kansiloli don inganta gudanar da ayyukan su na majalisar ƙaramar hukumar.
Gwamna Raɗɗa ya yaba wa shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Isah Miqdad AD Saude, bisa jajircewarsa da kuma rawar gani da yake takawa wajen aiwatar da ayyukan raya ƙasa, yana mai cewa irin waɗannan ayyuka na nuna gaskiya, kishin al’umma da kuma bin diddigin manufar gwamnatin jihar ta inganta walwalar jama’a.
Ya kuma jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da tallafawa shugabannin ƙananan hukumomi domin tabbatar da an isar da sauyi ga kowanne yanki na jihar Katsina.
Malam Dikko Raɗɗa wanda ya kammala ziyarar aiki a ƙananan hukumomin jihar ya kuma buɗe wasu manyan ayyuka da ɗan majalisar tarayya Hon Sani Danlami ya aiwatar a ƙaramar hukumar da suka haɗa da asibitoci,hanyoyi da sauran su.
