Aminci a tsarin zaɓen Nijeriya: Shin na’urorin BVAS da IReV sun isa?

Spread the love

A taron masu ruwa da tsaki kan zaɓe da ƙungiyar ‘Nigeria Civil Society Situation Room’ ta shirya a Abuja kwanan nan, shugaban Hukumar Zaɓe ta ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya yi bayani cikin gaskiya kan ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da ke ci gaba da damun tsarin zaɓen Nijeriya: yadda ake haɗa fasahar zamani da gudanar da zaɓe. Jawabinsa, wanda ya fi karkata ga tsarin tantance masu kaɗa ƙuri’a na BVAS da kuma dandalin nuna sakamakon zaɓe na IReV, ya sake buɗe muhawara a matakin ƙasa kan yadda za a tabbatar da ingancin su a zaɓukan masu zuwa.

Lokacin da aka fara gabatar da waɗannan tsare-tsare, ’yan Nijeriya sun karɓe su da fatan alheri, duk da ɗan shakku. An ƙirƙiri na’urar BVAS ne domin kawar da matsalolin da suka daɗe suna lalata zaɓe, irin su kaɗa ƙuri’a fiye da sau ɗaya, kwaikwayon masu kaɗa ƙuri’a da kuma cuɗanyar sakamako ta hannu. IReV kuma an tsara ta ne domin bai wa jama’a damar ganin sakamakon daga rumfunan zaɓe kai tsaye, ta yadda kowa zai sa ido. A haɗe, an yi tsammanin za su buɗe sabon babi na zaɓe na gaskiya da adalci. Sai dai zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ya fallasa matsalolin aiki da na ababen more rayuwa da suka girgiza amincewar jama’a, suka kuma tayar da shakku kan sahihancin tsarin.

Farfesa Amupitan bai guje wa amincewa da waɗannan na’urori ba. Ya nuna raunin hanyoyin sadarwa da ƙarancin isasshen intanet, musamman a yankunan karkara da wuraren da ke da wahalar isa, a matsayin manyan ƙalubalen aiwatar da fasahar zaɓe yadda ya kamata. Da rumfunan zaɓe sama da 176,000 a faɗin ƙasar, da dama daga cikinsu na cikin ƙauyuka masu nisa, ɗora sakamako kai tsaye ya kasance babban aiki mai wahala. Kamar yadda ya jaddada, fasaha ba za ta yi tasiri ba sai idan akwai ginshiƙan da za su ɗauke ta.

Duk da haka, ya dace a gane irin ci gaban da aka samu. Idan aka kwatanta da shekarun baya masu cike da sace-sacen akwatunan zaɓe da murƙushe nasara a idon jama’a, shigar BVAS da IReV ya nuna gagarumin sauyi. Sun rage wasu nau’o’in maguɗi, kuma aƙalla sun ɗaga ma’aunin gaskiya. Ko da yake kamala ba a kai ba, bai dace a watsar da waɗannan nasarori gaba ɗaya ba.

ƙarfin jawabin Farfesa Amupitan ya ta’allaƙa ne a kan yadda ya fuskanci ƙuntatawar a sarari, yana kallon su a matsayin matsalolin da za a magance, ba hujjar ja da baya daga gyare-gyare ba. ƙudurin da ya nuna na ƙara haɗin gwiwa da Hukumar Sadarwa ta ƙasa da manyan kamfanonin sadarwa na nuna fahimtar cewa sahihin zaɓe a zamanin dijital na buƙatar haɗin kai fiye da INEC kaɗai. Ganowa da amincewa da matsala shi ne matakin farko na warware ta.

Haka kuma, INEC na da dama a gaba. Dokoki da kundin tsarin mulki sun ba ta ikon ɗauka da aiwatar da sabbin tsare-tsare na fasaha domin inganta sakamakon zaɓe. Wannan ’yanci ya kamata ya ƙarfafa hukumar ta yi tunani mai faɗi. Idan IReV, a halin da yake ciki, bai kai matsayin da ake so ba, bai kamata a ɗauke shi a matsayin abu da ba ya sauyawa ba. Fasaha na canjawa cikin sauri, kuma dole tsarin zaɓe ya tafi daidai da wannan canji.

Nijeriya ba ta rasa ƙwararrun masana fasaha ba. BVAS da IReV ayyuka ne na cikin gida, da ƙwararrun ’yan Nijeriya suka ƙirƙira, kuma ƙasar na da ɗimbin masana IT da za su iya inganta tsarin da ake da shi ko ƙirƙiro sabbi gaba ɗaya. Maimakon jingina da matsalolin ababen more rayuwa a matsayin uzuri na dindindin, ya kamata INEC ta zuba jari wajen ci gaba da gwaji, koyo daga kura-kurai da kuma ɗaukar nagartattun dabaru na duniya. Wasu dimokiraɗiyya sun fuskanci irin waɗannan ƙalubale, kuma babu dalilin da zai hana Nijeriya daidaita mafita da ta dace da yanayinta.

A tsakiyar wannan muhawara akwai gaskiya mai sauƙi amma mai ƙarfi: ’yan Nijeriya na son zaɓe mai sahihanci. Suna son tsarin da ƙuri’unsu ke da tasiri, zaɓinsu kuma ke da daraja. Tsarin zaɓe da jama’a ke ganin yana da gaskiya da amincewa zai ƙara yawan masu fitowa kaɗa ƙuri’a. Raguwar sha’awar zaɓe da ake gani a baya-bayan nan sakamakon rashin gamsuwa da ɓacewar amana ce. Idan aka dawo da amincewa, masu zaɓe za su dawo.

Gina tsayayyen tsarin hukuma a cikin INEC, tare da fasaha abin dogaro da ingantattun hanyoyin sa ido da lissafi, ba zaɓi ba ne; wajibi ne. Dimokiraɗiyya na bunƙasa ne idan jama’a sun yarda da hukumomin zaɓe, kuma ana samun wannan amincewa ne ta hanyar daidaito, buɗe ido da nuna ƙudurin gyara a aikace.

A ƙarshe, sahihin tsarin zaɓe mai aiki shi ne ƙashin bayan kowace dimokiraɗiyya. Yayin da Nijeriya ke ci gaba da tafiyarta ta dimokiraɗiyya, wajibi ne kowa ya bada gudunmawa. Sabbin fasahohi, gyaran hukumomi da ƙarfin siyasa dole su yi aiki tare domin mayar da INEC hukuma da ke jawo amincewa da girmamawa.

By ukarofi