Bambancin da ke tsakanin Hikayata da sauran gasa tamkar jami’a ce da kwaleji – Hafsat Sani Tanko 

Spread the love

Gasar Hikayata ita ce babbar gasar da babu kamar ta – Fadila Lamiɗo 

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

A bana Gasar Hikayata ta marubuta mata zalla da tashar BBC Hausa ta saba gabatarwa duk shekara ta cika shekara goma. A kowacce shekara kamar yadda muka saba gani, mata marubuta daga sassan duniya daban-daban, inda ake da Hausawa ko masu amfani da harshen Hausa, suna aikawa da labaransu, domin neman shiga gasar ƙirƙirarrun gajerun labarai ta Hikayata. A ƙarshen gasar ana fitar da gwaraza uku da labaransu suka yi fice, tare da jinjina ga rukuni na biyu na mutane goma sha biyu da suka yi bajinta wajen tsara labaransu.

A gasar Hikayata ta bana ma an fitar da sunayen gwaraza uku, waɗanda aka karrama su da shaidar yabo da kuma kuɗi mai tsoka, wanda zai karfafa musu gwiwa a harkar rubutun da suke yi, kuma iyalinsu su fahimci lallai rubutun da suke yi yana da rana sosai, musamman ma dai ga marubutan da suke da aure. An ɓullo da Gasar Hikayata ne domin ƙarfafa gwiwar marubuta mata su yi amfani da basirar su wajen fitar da matsalolin da al’ummar da suke tare da ita ke ciki, domin isar da saƙon da suke gabatarwa ga gwamnati da sauran masu riƙe da madafun iko, don a ɗauki matakin gyara. Ko kuma su al’umma su yi wa kansu karatun ta natsu, su canza yadda suke tunani da gudanar da al’amuransu, don samar da sauyi a rayuwarsu.

Malama Fadila Lamiɗo daga Jihar Kaduna, wacce sau uku tana shiga gasar Hikayata, ita ce ta zama Gwarzuwa ta Farko, tare da samun kyautar kuɗi har Naira miliyan ɗaya. Yayin da Jamila Lawal Zango ita ma daga Zariya a Jihar Kaduna ta zama Gwarzuwa ta Biyu, tare da samun kyautar kuɗi Naira dubu 750. Gwarzuwa ta Uku ita ce, Hafsat Sani Tanko daga Jihar Kano da ta samu kyautar Naira dubu 500. Waɗannan gwaraza an zaɓo su ne bayan ƙwarewa da suka nuna, da kuma tasirin da labaran su suka yi a wajen alƙalan Gasar Hikayata, daga cikin labarai fiye da 400 da aka shigar don neman cancanta da samun nasara a wannan gasa.

“Ranar da aka kira ni daga BBC Hausa cewa ina daga cikin waɗanda labaransu suka samu shiga mataki na ƙarshe na ruɗe sosai, daren ranar ban iya barci ba sam. Kuma har aka ɗauki kwanaki gani nake yi kamar mafarki nake zan farka.” Faɗila Lamiɗo kenan Gwarzuwa ta Farko take bayyana yadda ta ji da kiran farko da BBC suka yi mata. 

A cewar, Jamila Lawal Zango, wacce ta shiga gasar Hikayata sau shida, sai a wannan karon ta samu nasara da labarin ta mai suna ‘Gobena’, “Ji na yi tamkar a mafarki, domin nasarar ta zo mini a lokacin da na sare nake ganin akwai wasu marubutan da suka fi ni jajircewa da son su ga sun ci gasar. Wannan ya sa har lokacin da aka kira ni har na tafi nake ganin kamar mafarki.”

Gwarzuwa ta Uku, Hafsat Sani Tanko, ita ce za a ce ta shiga wannan gasa da ƙafar dama. Domin kuwa wannan shi ne karon farko da ta shiga cikin Gasar Hikayata da labarinta mai taken, ‘Samarin Shaho’. Sannan za a iya cewa idan ana gadon rubutu to, Hafsat ýargado ce, domin kuwa mahaifiyarta tsohuwar marubuciya ce, wacce har littattafai ta buga. Sai dai a cewarta, dogaro ga Allah da tsananta addu’a su ne sirrin nasararta ba don ta yi gadon rubutu ba.

Fadila Lamiɗo da ta zama Gwarzuwa ta Farko, tsohuwar marubuciya ce wacce ta rubuta littattafai sun kai 16, fitattu daga cikinsu su ne, ‘Bugun Zuciya’ da labarin ‘Kowanne Bakin Wuta’.  Labarin da ta samu nasara da shi mai suna, ‘Tsalle ɗaya’, labari ne akan wata matar aure mai yara ƙanana, wacce yunwa ta jefata a cikin wani mawuyacin hali, har ta ke ganin mutum da gishirinsa in ya ga dama ko ƙaho sai ya dafa. Duk da cewa makusantan ta sun yi ta nusar da ita muhimmancin neman na kai tare da ɗora ta akan sana’o’i daban-daban. Amma saboda rashin jajircewarta ta bi hanyar da bata dace ba, don nema wa kanta da yaranta mafita, abin da ya shigar da ita har ta shigo da ‘yar da ita kanta bata da tabbacin ubanta, tsakanin mijin aurenta da wani namijin a waje. Daga ƙarshe dai ta tsinci talatarta a Laraba, domin garin neman gira dai ta rasa ido, inda har mijnta mai nuna halin ko-in-kula akan iyalinsa ya samu tsaraba, don haka gaba ɗayansu ido ya raina fata.

Labari na biyu kuwa shi ne labarin, ‘Gobena’ na Jamila Lawal Zango, wanda bayan shi ta rubuta wasu littattafai biyar da ta fitar da su a yanar gizo. Fitacce daga cikin littattafanta shi ne, ‘Wasu Mazan’, wanda shi har bugawa ma aka yi. Labarin ‘Gobena’, labari ne akan wata budurwa da mahaifiyarta ta ci burin ta gina mata ingantacciyar rayuwa ta hanyar ba ta tarbiyya da ilimi, amma sai buduwar ta watsa mata ƙasa a Ido, ta hanyar amfani da kafar sada zumunta tana rawa da shigar baɗala tana yin duk abin da zai jawo mata suna, wanda a ƙarshe har baƙincikin hakan ya sanya mahaifiyarta ta mutu. A ƙarshe yarinyar ta haɗu da mummunar makoma a gobenta. Labarin ya yi tsokaci game da yadda mata suke raye-raye a soshiyal midiya, don su samu duniyar shahara ba tare da sun yi duba ga gobensu ba.

Gwarzon labari na uku shi ne ‘Samarin Shaho’, wanda tun daga sunansa yake bayyana saƙon da yake ɗauke da shi, da ya shafi wata halayya da matasa suka ɓullo da ita a wannan zamani, inda za ka ga saurayi da budurwa an sha soyayya, amma idan ƙaddara ta raba su, a maimakon su miƙa wa Allah lamarin su, sai wasu samarin su cigaba da hira da tsohuwar masoyiyarsu wacce take gidan mijinta. Labarin yana nuna yadda jarumin labarin Akram, ya hure wa budurwarsa Amira kunne, bisa cewa idan mijinta Usman ya saketa to, shi yana nan kan bakarsa, sai ya aureta. Daga nan ta tsiri bijire wa umarnin mijinta, har ya saketa, kuma daga ranar ba ta sake ganin saurayinta Akram ba, sai sakon katin ɗaurin aurensa da kawarta da ta gani. 

Dukkan waɗannan marubuta sun nuna hikima da jajircewa wajen shiga wannan gasa da ake tunanin samun nasara a Hikayata shi ne ƙurewar nasara a rubutu. A cewar Fadila, “Gasar Hikayata ita ce babbar gasa wacce babu kamarta a dukkanin gasannin da ake sawa a tsakanin marubuta adabin Hausa.” Wannan ra’ayi nata ya zo daidai da na Hafsat Sani Tanko, wacce ta ce bambancin da ke tsakanin Hikayata da sauran gasanni tamkar Jami’a ce da Kwaleji, darajarsu ba ɗaya ba ce. “Kai, BBC fa duniya ce! Ba wai ina kushe sauran gasannin Hausa ba ne, duk ƙanƙantar gasa alheri ce ga marubuta, amma dai BBC uwa ce ma ba da mama.”

Shawarar su ga marubuta mata masu burin shiga wannan gasa da waɗanda suka daɗe suna gwadawa ba su yi nasara ba, ita ce a kiyaye ƙa’idojin rubutu da dokokin gasar, a yi rubutu kan jigo mai kyau da zai ja hankalin alƙalan gasa. Sannan su raka da addu’a. Hafsat ta ce, “A fahimtata duk ƙwarewarki da daɗewarki a rubutu ba za su kai ki ga samun nasara a wannan gasa ba, sai kin dage da addu’a. Sannan ki samu ƙwarin gwiwa kan cewa lallai Allah ne mai ba da nasara, ba wani mutum ko wani dalili ba. Domin ni ban taɓa shiga Gasar Hikayata ba sai a wannan karon!”

By ukarofi