Fitaccen zakaran dambe na duniya, Anthony Joshua, na tunanin ja gefe daga harkar damben ƙwararru bayan tsira daga wani mummunan hatsarin mota da ya yi sanadiyyar rasuwar wasu muhimman mutane biyu a tawagarsa, inji iyalansa.
Kawun Joshua, Adedamola Joshua, ya bayyana wa manema labarai cewa ɗan damben mai shekaru 36 ya riga ya sanar da iyalinsa a sirrance game da shawarar da yake tunanin ɗauka, biyo bayan hatsarin da ya auku makon jiya a Nijeriya.
“Abu mafi muhimmanci shi ne ya ce ya bar dambe,” inji kawun nasa yayin wata ziyara da aka kai gidan iyali a Sagamu, jihar Ogun. “Wannan ne ya sa muke jin daɗi, domin duk lokacin da yake shiga filin dambe, zukatanmu kan shiga tashin hankali. Idan aka kwantar da shi a wasa, kamar an cire mana zuciya. Raunin tunani ya yi yawa.”
Ya ƙara da cewa, iyalin sun amince da shawarar Joshua na yin ritaya, ganin yadda ya kai kololuwa a aikinsa. “Yanzu da ya ce zai bar wasa tun yana kan ganiyarsa, mun ji daɗi,” inji shi, yana tabbatar da cewa Joshua da kansa ne ya sanar da su hakan.
Anthony Joshua ya tsira ne daga hatsarin mota mai tsanani da ya rutsa da su a babbar hanyar Legas–Ibadan, inda motar Leɗus SUV da suke ciki ta buɗe da wata babbar mota da ta tsaya a hanya. A hatsarin, kocin ƙarfin jiki da motsa jiki na Joshua, Sina Ghami, da kuma mai horar da shi na ƙut-da-ƙut, Latif ‘Latz’ Ayodele, sun rasu nan take. Su biyun sun daɗe suna cikin makusantan tawagar Joshua, kuma sun zo Nijeriya tare da shi domin ziyarar iyali.
Joshua ya samu raunuka marasa tsanani, inda aka ceto shi daga motar aka kai shi asibiti domin jinya. Rahotanni sun ce dan damben ya ɗauki alwashin tallafa wa iyalan waɗanda suka rasu har tsawon rayuwarsu, a wani mataki da ke nuna tsananin amincinsa ga mutanen da ke kewaye da shi.
Wani majiyi daga tawagarsa ya shaida wa jaridar The Sun ta Birtaniya cewa Joshua mutum ne mai tsananin biyayya ga abokansa da iyalansu. “AJ ba ya mantawa da mutanensa. Zai tsaya tare da iyalan Sina da Latz har abada,” inji majiyar.
