
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A yau Asabar ne Shugaba Yoweri Museveni na ƙasar Uganda ya sake lashe zaɓe a karo na bakwai bayan gudanar da zaɓen, wanda aka fuskanci barazanar rikice-rikicen siyasa.
An kuma katse layin intanet da fuskantar tashin-tashina, inda masu sanya ido suka ce kame da garkuwa sun sanya firgici acikin al’ummar ƙasar.
Museveni mai shekaru 81 ya lashe zaɓen ne da kaso 71.65 na ƙuri’un da aka kaɗa a ranar Alhamis, kamar yadda hukumar zaɓen ƙasar ta bayyana.
Rahotanni sun bayyana cewa aƙalla mutane goma ne suka rasu yayin da ɓangaren adawa da ƙungiyoyin al’umma suka fuskanci barazanar ikon gwamnati.
Shugaban ƙasar ya doke abokin hamayyarsa, Bobi Wine mai shekaru 43, wanda ya samu kaso 24.72 sannan ya yi ikirarin jami’an tsaro sun kai samame gidansa yayin yake halin ɓoya.
Wine ya bayyana cewa ya fuskanci matsi tun farkon shigar sa harkokin siyasa, inda an sha kama shi musamman gabanin fara tsayawarsa takarar shugaban ƙasa a 2021.
