PTDF 2026: Gwamnatin Nijeriya ta buɗe damar neman tallafin gurbin karatu a ƙasashen waje

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ta sanar da buɗe damar neman tallafin karatu a ƙasashen waje na Asusun Ci gaban Fasahar Man Fetur (PTDF) na shekarar 2026, ga ’yan Nijeriya da suka cika sharuɗɗan shiga shirye-shiryen digiri na biyu da na uku a jami’o’in ƙetare.

Sanarwar na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da PTDF ta fitar a ranar Litinin, inda hukumar ta bayyana cewa shirin zai rufe karatun digiri na biyu (MSc) da digiri na uku (PhD) a ƙasashe irin su Birtaniya, Jamus, Faransa da Malaysia.

A cewar PTDF, wannan shirin tallafin karatu na ƙasashen waje na daga cikin ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na gina ƙwarewar ‘yan ƙasa da kuma harkar basirar cikin gida a bangaren mai da iskar gas, da kuma wasu fannoni masu alaƙa da ci gaban ƙasa.

Hukumar ta bayyana cewa shirin ya mayar da hankali ne kan ɗaliban da ke karatu a fannoni da suka dace da masana’antar man fetur, ciki har da injiniyanci, ilimin ƙasa (geosciences), nazarin muhalli da kuma fannonin gudanarwa, da sauransu.

PTDF ta ce ɗaliban da aka zaba za su amfana da cikakken tallafi wanda ya ƙunshi biyan kuɗin makaranta, masauki, tikitin jirgin sama, inshorar lafiya da kuma alawus-alawus na kowane wata tsawon lokacin karatunsu.

Hukumar ta kuma bayyana sharuɗɗan shiga, inda ta ce masu neman tallafin karatun digiri na biyu dole ne su kasance da sakamakon Second Class Upper a fannin da ya dace. Haka kuma, masu neman tallafin digiri na uku ana sa ran sun kammala aikin yi wa ƙasa hidima (NYSC) tare da ingantaccen tarihin karatu da shaidar digiri na gaba da sakamako mai kyau.

PTDF ta shawarci masu sha’awa da su nemi shiga shirin ta hanyar shafin yanar gizon tallafin karatu na hukuma, tare da jan hankali cewa neman shirin kyauta ne ba tare da biyan kuɗi ba. Hukumar ta kuma gargaɗi ‘yan ƙasa da su yi hattara da ‘yan damfara da ke fakewa da sunan PTDF domin yaudarar jama’a.

Gwamnatin Tarayya ta buƙaci ’yan Nijeriya da suka cancanta da su yi anfani da wannan dama, tana mai jaddada cewa shirin tallafin karatu na PTDF na daga cikin manyan dabarun bunƙasa jari na bil’adama a ɓangaren makamashi da ci gaban ƙasa baki ɗaya.

By ukarofi