Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta yi tir da kisan kiyashin Kwara da dukkan ayyukan ta’addanci

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi (MWL) ta yi alla-wadai da harin ‘yan ta’adda da ya yi sanadiyyar mutuwar mazauna garin Woro a Jihar Kwara, inda aka yi wa mutane da dama kisan gilla da raunata wasu.

A wata takarda da ta fitar a Babbar Sakatariyarta da ke Makka, MWL ta bayyana harin a matsayin mummunan ta’addanci ga al’ummar musulmi, tana mai tir da nuna ƙiyayyarta ga dukkan ayyukan ta’addanci a sassan Nijeriya.

MWL ta ce tana tare da Nijeriya a wannan lokaci na alhini tare da goyon bayanta akan ƙoƙarin da take yi wajen magance matsalolin dukkan barazanar tsaro da ƙasar ke fuskanta da ke addabar zaman lafiyar al’umma.

Ƙungiyar ta nanata aniyarta ta ƙin dukkan ayyukan rikice-rikice da ta’addanci a dukkan manufofinsu, tana mai jajenta wa waɗanda iftila’in ya afka wa da iyalansu.

Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi, wadda ke da ofishinta a Makka, ta sha maimaita adawarta ga ayyukan ta’addanci da al’amuran da suka shafi tsatstsauran. A madadin haka, take kira ga bin tsarin tattaunawa, zaman lafiya da girmama rayuwar ɗan-adam a matsayin ginshiƙan warware matsalolin tsaro a matakin duniya.

A ranar Laraba aka samun rahoton kisan mutane 170 daga wasu da ake zargin ‘yan ta’adda yankin Sahel ne a ƙauyen Woro da ke Ƙaramar Hukumar Kaiama da ke Jihar Kwara.

An ruwaito cewa, ‘yan ta’addar suna da alaƙa da tsagin Sadiku na ƙungiyar Boko Haram, waɗanda suka shiga yankin a daren Talata tare da ƙaddamar da mummunan harin.

By Babaji