Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Jam’iyyar APC ta yi watsi da ƙaryata zargin da jam’iyyar ADC ta yi mata na tilasta ma’aikatan gwamnati wajen yin rajistar shaidar zama ‘yan APC a rajistar da jam’iyyar ke yi a faɗin Nijeriya.
A cikin jawabin da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar APC ya sa wa hannu, Feliɗ Morka, ya ce, fargaba da tsoro ne suka sa ADC furta wannan zargi saboda irin dubban mutanen da suke zuwa yin rajistar shiga jam’iyyar.
A ranar Lahadi ce ADC, ta hannun sakataren yaɗa labaranta na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ta nuna damuwarta game da rahotanni da ke nuna cewa ana tilasta wa ma’aikatan gwamnati a faɗin Nijeriya domin su yi rajistar zama mambobin jam’iyyar APC.
Jam’iyyar adawar ta bayyana matakin da “tilasta shiga jam’iyyar (APC)” inda ya ce tilasta wa ma’aikatan gwamnati su shiga wata jam’iyya abu ne da ya saɓa wa kundin tsarin mulki da ya tabbatar da ‘yancin ɗan’adam na ra’ayi kan shiga wata ƙungiya wanda kuma tilasta mus barazana ce ga tsarin tsama ‘yan ba ruwana ga ma’aikatan gwamnati.
ADC ta yi gargaɗin cewa idan rahotannin suka zama gaskiya, to ta tabbatar an yi amfani da ƙarfi da ƙoƙarin tattara bayanai al’umma wanda barazana ce ga ‘yancin ɗan’adam.
A yayin da yake mayar da martani, Morka ya ce, zargin da ADC ke yi na da alaƙa ne da “irin gagarumar nasara” na rajista ‘ya’yanta wanda aka ɓullo a matsayin wani tsarin tattara bayanan ‘yan jam’iyyar ta hanyar dijital.
Ya kuma ƙara da cewa jam’iyyar adawa na waɗannan kalamai ne a matsayin wata dabara ta yaɗa labaran ƙarya inda ya buga misali wata rajista ta ƙarya da aka yi wa wani fitaccen jagoran ‘yan bindiga a matsayin ɗan APC.
Jam’iyya mai mulki ta ce, yin rajistar ta intanet da ake yi wa ‘ya’yanta ba wajibi ba ne. Sai dai ya samu karɓuwa sakamakon miliyoyin ‘yan Nijeriya da rahotanni suka nuna sun yi rajistar bisa raɗin kansu.
Sakamakon yawan mutanen da suke fitowa rajistar, APC ta ƙara wa’adin rufewar da ta ayyana daga 31 ga watan Janairu zuwa 8 ga watan Fabarairu.
A cewar jam’iyyar, irin wannan tururuwa da al’umma ke yi na nuna suna yi saboda raɗin kansu a maimakon zargin da ADC ke yi na ana tilasta al’umma. Ya ce, sukar wata dabara ce ta ƙarya guiwar mutane daga zuwa rajistar.
APC ta jaddada aniyarta ta ci gaba da ɓullo da hanyoyin zamanantar da ayyukanta, tana mai bayyana cewa rajistar da ake kan yi an tsara ta ne domin zamanantar da tsarin jam’iyyar gabanin zaɓuka da ƙarfafa dimokradiyya a cikin gida.
