Tinubu zai halarci taron masunta a Kebbi – Gwamna Idris

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwama Nasir Idris na Jihar Kebbi ya sanar da cewa Shugaba Bola Tinubu zai je ziyarar aiki ta kwana biyu a jihar domin ƙaddamar da muhimman ayyukan ci-gaba da gwamnatinsa ta gudanar.

Manhaja ta ruwaito cewa, gwaman ya kuma ce Shugaban ƙasar kuma zai halarci babban taron masu sana’ar kamun kifi da al’adu na ƙasa-da-ƙasa da aka saba yi duk shekara a garin Argungu, wanda zai gudana daga ranar 11 zuwa 14 ga Fabrairu.

Da yake magana a taron karɓar wasu ‘yan siyasa daga Ƙaramar Hukumar Jega da suka koma Jam’iyyar APC, Gwamna Idris ya yi kira ga ‘yan ƙasa da su yi cincirindo wajen marabtar Tinubu bisa karamci.

Gwamnan ya bayyana cewa, taron al’adar zai samu halartar mutane daga ciki da wajen Nijeriya.

Game da waɗanda suka koma APC, Idris ya yaba wa matakin nasu tare da tabbatar musu da cewa za a mu’amalance su kamar kowane mamban jam’iyyar ba tare da la’akari da lokacin shigarsu ba.

Ya kuma ƙara da cewa, gwamnatinsa ta aiwatar da manyan ayyuka ci-gaba a Ƙaramar Hukumar Jega, yana mai jaddada ƙudirinsa na samar da ci-gaba a dukkan sassan jihar.

By Babaji