
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arziƙin Dijital, Isa Ali Pantami, ya ce da dama daga cikin huɗubobinsa na baya akan dimukraɗiyya da siyasa an jirkita ko sauya su daga haƙiƙanin abin da yake nufi.
Pantami ya bayyana haka ne a wata hira da BBCHausa a ranar Asabar yayin da ake tsaka da cece-kuce akan sabunta zamansa mamba a jam’iyyar APC.
A yayin haka ne tsohon ministan ya ce yana gudanar da harkokin siyasa a tsawon sama da shekaru 20, lamarin da ya sa wasu masu sharhi suka ce ya saɓa wa matsayinsa na baya akan shiga siyasa.
Da yake tsokaci akan al’amarin, malamin addinin ya ƙalubalanci masu yaɗa bidiyoyin huɗubobin da su fitar inda ya yi ikirarin haka.
Ya yi zargin cewa da dama daga cikin biliyoyin an jirkita su, sannan an ɗora su ba a gurabensu ba.
Ya yu tsokaci akan wani da ake yaɗawa da yake cewa ba ya halartar taron siyasa, inda ya ce ya yi wannan furucin ne sama da shekaru 20 da suka gabata a lokacin da yi muhawara akan halascin ilimin boko, aiki a gwamnati da dimukraɗiyya a musulunci.
Ya ƙara da cewa, kasancewar mutum bai zama ɗan siyasa a yau ba,ba shi ke nuna kuma a gobe ba zai shiga harkar ba, ko kuma kwatakwata ba zai taɓa sauya matsaya ba.
