Fadar Shugaban Ƙasa ta yi wa Atiku shaguɓe kan komawar Fintiri APC

Spread the love

Fadar Shugaban Ƙasa ta yi wa tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar shaguɓe bayan sauya sheƙar Gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri zuwa jam’iyyar APC, tana mai cewa matakin babbar koma-baya ne ga burinsa na takarar shugaban ƙasa.

Kakakin Shugaban Ƙasa Bayo Onanuga ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafin sada zumunta na X a yau Juma’a, inda ya ce sauya sheƙar Fintiri na nuna cewa Atiku ba shi da cikakken farin jini a jiharsa ta asali.

Sanarwa ya ƙara da cewa “gwamna Finitri ya ɗauke wa Atiku duk wata ƙarfinsa ta jiharsa zuwa jam’iyyar shugaba Bola Tinubu ta APC.

A cewar sanarwar, “ɗan takarar da ba shi da ƙarfi a garinsa ba zai iya tallata kansa ga sauran yankuna ba.”

Fadar ta kuma shawarci Atiku da ya yi tunanin yin ritaya daga siyasar jam’iyya, tare da komawa “gidansa na biyu” da ke Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa musamman a birnin Dubai.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa yayin da zaɓen shugaban ƙasa ke ƙaratowa cikin ƙasa da shekara guda, sauya sheƙar Fintiri na daga cikin manyan matsalolin da ka iya shafar shirin Atiku na sake tsayawa takara, tana mai cewa wannan lamari babbar barazana ce ga burinsa na siyasa.

By Babaji