
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sufeto Janar na Rundunar ‘Yan Sanda, Olatunji Disu, ya umarci kwamishinonin hukumar na jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya (FCT) da ke faɗin Nijeriya da su ƙara tsaurara sanya ido da tattara bayanan sirri, sakamakon rikicin Gabas ta Tsakiya da ke cigaba da ƙamari tsakanin Iran da Amurka da Isra’ila.
Wannan umarni ya biyo bayan zanga-zangar da mambobin ƙungiyar ‘yan Shi’ah ta ‘Islamic Movement in Nigeria (IMN)’, suka gudanar a Jihar Neja ta nuna adawa da kisan Jagoran Musulunci na Iran, Ali Khamenei a hare-haren haɗin-gwiwa da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar.
Rahotanni sun ce Iran ta mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami zuwa wurare da suka haɗa da sansanonin da ke ɗauke da sojojin Amurka a ƙasashen Gabas ta Tsakiya d suka haɗa da Bahrain, UAE, Saudiyya da Ƙatar.
A ranar Lahadi ne ɗaruruwan ‘yan IMN suka fito kan titunan garin Minna ɗauke da tutocin Iran da alluna masu ɗauke da saƙonni kamar “We Stand With Iran” da “Free Iran”, tare da rera taken nuna goyon bayan Iran da adawa da Amurka da Isra’ila.
A sanarwar da ƙungiyar ta fitar, ta bayyana alhininta akan abin da ta kira da “shahadar Sayyid Ali Khamene’i” da kuma jaddada goyon baya ga ‘yan ƙasar.
Kakakin Rundunar ‘yan Sanda, Benjamin Hundeyin, ya ce rundunar ta tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa tsaron ƙasa na nan daram, kuma an ƙarfafa matakan tsaro na sa-kai da tattara bayanan sirri a faɗin ƙasar, kamar yadda ya faɗa a wata takarda.
Olatunji Disu ya bayyana rundunar na haɗa kai da sarakuna da shugabannin addini, tare da ƙara yawan sintiri a wuraren ibada da sauran wuraren taruwar jama’a domin hana duk wata yunƙuri ta haddasa rikici ko rarrabuwar kawuna a sassan Nijeriya.
Haka kuma, ya yi gargaɗin cewa Nijeriya ba za ta zama fagen shigo da rikice-rikicen ƙasashen waje ba, saboda haka duk wanda ya yi yunƙurin tayar da rikicin addini ko na aƙida daga waje, zai fuskanci hukuncin da doka ta tanada.
Kazalika, ya kirayi jagororin al’umma da su cigaba da wayar da kan jama’arsu akan harkokin zaman lafiya, tare da kira ga ‘yan ƙasa su kasance cikin nitsuwa, tare da kiyaye doka, yana mai shawartar su da su riƙa kai rahoton duk wani abin zargi.
