
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta bada belin Abubakar Malami, tsohon Antoni-Janar na ƙasa (AGF), matarsa Asabe Bashir da kuma ɗansa Abdulaziz Malami.
Mai shari’a Joyce Abdulmalik je ta yi hukuncin a yau Juma’a inda ta yanke cewa kowane ɗaya daga cikinsu zai biya Naira miliyan 200 da kuma mutane biyu da za su iya tsaya masu aka belin.
Haka kuma, kotun ta buƙaci da su bada fasfo ɗinsu a ajiye shi a gaban ƙuliya har zuwa lokacin kammala shari’ar.
Ga yadda sharuddan belin nasu yake dalladalla:
- Kowanne zai bada beli na ₦200,000,000
- A kawo mutane biyu masu ƙarfi da za su tsaya.
- Ɗaya daga cikinsu wajibi ne ya mallaki gida a Maitama ko Asokoro a Abuja
- Dole su miƙa fasfo na ƙasashen waje ga kotu
Sai dai kotun ta umarce su da su cigaba da zama a hannun hukuma har sai sun cika dukkan sharuddan belin.
Ana tuhumar Malami da iyalan nasa ne da laifukan badaƙalar kuɗaɗe da suka kai jimillar biliyan ₦8.7, zarge-zargen da suka janyo shari’a akansu.
