Ramadan: Abba Minista ya tallafa wa malamai da limamai 1,000 da kayan abinci 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Shahararren mai taimakon jama’a, Alhaji Abba Minista, ya raba kayan abinci ga kimanin malaman addinin Musulunci da limamai 1,000, domin tallafa musu a wannan lokaci na watan azumin Ramadan tare da rage musu raɗaɗin halin ƙuncin da ake ciki.

An gudanar da rabon tallafin ne a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin Alhaji Abba Minista na ci gaba da tallafa wa marasa ƙarfi da sauran sassan al’umma masu buƙatar taimako.

Malaman addini da limaman da suka amfana da tallafin, waɗanda suka fito daga sassa daban-daban na al’umma, sun nuna matuƙar godiyarsu kan wannan taimako da suka ce ya zo a daidai lokacin da ake buƙatarsa.

Sun bayyana cewa kayan abincin da aka ba su zai taimaka musu da iyalansu wajen gudanar da ibadar azumi cikin sauƙi a wannan wata mai alfarma.

Da yake jawabi yayin rabon tallafin, Alhaji Abba Minista ya jaddada muhimmancin taimakon juna, haɗin kai da tausayi a tsakanin al’umma, musamman a cikin watan Ramadan wanda ke ƙarfafa ayyukan alheri da kula da marasa galihu.

Ya kuma buƙaci malaman addinin Musulunci da limamai da su ci gaba da yi wa ƙasa addu’ar samun zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaba mai ɗorewa.

A cewarsa, addu’o’i da hadin kan al’umma na da muhimmiyar rawa wajen tabbatar da ci gaban ƙasa da zaman lafiya a cikin al’umma.

Alhaji Abba Minista dai ya shahara wajen gudanar da ayyukan alheri da tallafawa mata, matasa da marasa ƙarfi, ba kawai a lokacin Ramadan ba har ma a sauran lokutan shekara.

Ayyukan jin kai da yake gudanarwa sun ci gaba da kawo sauyi mai kyau a rayuwar al’umma a sassa daban-daban na ƙasa.

By ukarofi