Gwamnatin Kano ta kammala shirin gurfanar da matasan da ake zargi da kisan mace da ’ya’yanta shida

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa ta kammala dukkan shirye-shiryen gurfanar da wasu matasa da ake zargi da hannu a kisan wata matar aure da ’ya’yanta shida a gaban Babbar Kotun Jiha domin fara shari’arsu.

An bayyana hakan ne a ranar Laraba lokacin da gwamnatin jihar ta gabatar da takardun tuhuma a gaban kotun majistiri da ke No-man’s-land a Kano, kan wasu matasa uku da ake zargi da hannu a mummunan kisan da ya faru a Unguwar ɗorayi Chiranchi.

Babban Sakataren Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano, Barrista Salisu Muhammad Tahir, ya shaida wa kotu cewa gwamnati ta kammala bincike tare da rubuta cikakken takardar tuhuma domin gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotun da ke da hurumin sauraron shari’ar.

Ya ce daga cikin mutanen da aka gurfanar akwai wanda aka wanke daga zargin kisan kai, sai dai ana zarginsa da hannu a wani lamari da ya shafi zargin yi wa wata yarinya fyaɗe, wacce daga bisani ta rasu bayan an zarge su da ƙwaƙule mata idanu.

Waɗanda aka gurfanar a gaban kotun sun haɗa da Umar Auwal, Yakubu ɗayyabu, Isyaku Yakubu da Umar Ali, inda ake tuhumarsu da haɗa baki da aikata kisan kai a unguwar ɗorayi.

A cewar takardar tuhumar, ana zargin matasan da haɗa baki wajen kashe mutane a wasu unguwanni daban-daban, bisa zargin aikata tsafi.

Daga cikin waɗanda ake zargin sun kashe akwai wata mata tare da ’ya’yanta shida a unguwar ɗorayi, sannan akwai wata mata da abokiyar zamanta da ake zargin an kashe su a unguwar Tudun Yola.

Haka kuma ana zargin matasan da hannu a wani lamari da ya shafi wata karamar yarinya da aka ce an yi mata fyaɗe kafin daga bisani aka kashe ta.

Lauyoyin gwamnatin jihar sun shaida wa kotu cewa an riga an kammala rubuta tuhume-tuhumen da ake yi wa matasan, domin a gurfanar da su a gaban Babbar Kotun Jiha wadda ke da hurumin ci gaba da sauraron shari’ar.

By ukarofi