Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Sojojin rundunar sojin ƙasa ta Nijeriya sun hallaka sama da ’yan ta’adda 60 a garin Mallam Fatori da ke ƙaramar hukumar Abadam a jihar Borno.
Rahotanni sun nuna cewa daga cikin waɗanda aka kashe akwai wasu manyan kwamandojin ƙungiyar Boko Haram/ISWAP da suka shahara wajen kai hare-hare.
Rundunar sojin ta bayyana cewa ’yan ta’addan sun taso ne daga yankin Duguri suna tafiya a ƙafa, tare da samun goyon bayan jiragen sama marasa matuƙi masu ɗauke da makamai, domin kai hari kan sansanin Bataliya ta 68.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Operation Hadin Kai, Sani Uba ya fitar a ranar Laraba, ya ce sojoji sun gano motsin ’yan ta’addan da wuri, inda suka yi gaggawar mayar da martani da ƙarfin wuta mai yawa.
Ya ce: “A cikin wani tsari mai kyau da aka shirya, sojoji tare da haɗin gwiwar rundunar sojin sama sun fatattaki maharan, inda suka hallaka sama da ’yan ta’adda 60 ciki har da wasu fitattun kwamandoji.
“Artabun mai tsanani ya tilasta sauran ’yan ta’addan tserewa cikin rudani zuwa yankin Arege.”
Uba ya ƙara da cewa sojoji sun fara bin sawun waɗanda suka tsere domin kamo su ko hallaka su, yayin da ake amfani da na’urorin leƙen asiri da sa ido domin dakile yunkurinsu na sake taruwa.
Ya jaddada cewa rundunar sojin Nijeriya na da ƙudirin ci gaba da kai farmaki kan ’yan ta’adda, tare da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin ƙasar nan.
Wannan nasara na zuwa ne kwanaki biyu bayan wasu hare-haren kunar bakin wake da suka auku a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, inda akalla mutane 23 suka mutu, yayin da 108 suka jikkata.
A ranar Talata, Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci shugabannin tsaro da su koma Maiduguri domin sa ido kai tsaye kan halin da ake ciki.
Shugabannin tsaron sun isa sansanin sojin sama da ke Maiduguri, inda kwamandan rundunar Operation Hadin Kai ya tarbe su, kafin su wuce hedikwatar rundunar domin gudanar da taro.
Daga bisani, babban hafsan tsaro ya duba girmamawar da aka yi masa, sannan ake sa ran za su gana da sojojin da ke gaba, jami’an gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki domin tattauna hanyoyin magance sake yawaitar hare-haren ’yan ta’adda a yankin.
Hare-haren da aka kai a ranar Litinin sun jefa tsoro da fargaba a zukatan al’ummar Maiduguri, duk da cewa an shafe wasu shekaru ana samun dan kwanciyar hankali.
Sai dai rundunar ’yan sanda ta jihar Borno ta ce zaman lafiya ya fara dawowa a Maiduguri bayan hare-haren.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sanda, Kenneth Daso, ya shaida wa manema labarai cewa jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro, yayin da ake bincike kan lamarin.
