Yadda muka sake fasalin sufurin jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna – Modibbo

Spread the love

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Tun bayan hatsarin jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna, wanda ya faru a watan Agusta na 2025, al’umma da dama sun faɗa fargabar shiga jirgin bayan dawowarsa aiki. Blueprint Manhaja ta kai ziyarar gani da ido a tashar jirgin ƙasan tare da tattaunawa da ko’odineta mai kula da sufurin Abuja zuwa Kaduna, ALHAJI MUHAMMAD IBRAHIM MODIBO, don samar wa masu karatu amsoshin tambayoyinsu tare da jin irin matakan da aka ɗauka, don ganin irin haka ba ta sake kasancewa ba. Ga yadda tattaunawar ta kasance tare da Editan Blueprint Manhaja, NASIR S. GWANGWAZO:

MANHAJA: A watannin baya kaɗan wannan jirgin ya samu hatsari akan hanyarsa ta zuwa Kaduna, wanda ya kawo ɗan tsaiko. Yanzu da ya kasance jirgin ya dawo kan aiki waɗanne irin canje-canje ne aka samu?

MODIBBO: To ƙorafe-ƙorafen da aka samu na farko dai kwastomominmu sun mana ƙorafi kan ƙarancin tafiyar da muke samarwa. Kasancewar bayan dawowarmu daga wannan hatsari, muna tafiya biyu ne kawai, wato daga Abuja zuwa Kaduna, da kuma Kaduna zuwa Abuja. To, kasantuwar mafi yawan masu shiga jirgin ma’aikata ne, waɗanda ke barin Abuja ranar Juma’a da yamma, su dawo Litinin da safe, don haka wanda muke yi ba ya isar su. Kuma alhamdu lillahi MD namu Dakta Kayode Ofefa ya yi namijin ƙoƙari, inda ya yi amfani da ilimin da yake da shi kan harkar sufuri ya samar da mafita kan wannan buƙata, wato aka samar da ƙarin tafiya ɗaya yanzu. Yanzu idan ka lura abinda muka ƙara a cikin tafiyar jirgin shi ne ranar Juma’a da Lahadi jirgin zai taso sau biyu daga Abuja. Daga Kaduna kuma sau ɗaya. Sannan kuma Asabar da Litinin jirgin zai baro Kaduna sau biyu, yayin da zai baro Abuja sau ɗaya. Hikimar yin hakan kuwa shi ne, samarwa ma’aikata ko masu kwangila da sauransu damar iya shige da fice ba tare da matsala ba.

Bari mu koma kan hatsarin, wanda ya faru a watan Agustan bara. Wane irin tanadi aka yi, don ganin an kauce wa ƙara faruwar sa?

To, shi abu irin wannan yana faruwa ne bisa ƙaddara ba wai abinda aka so ya kasance ba, amma duk da haka a matsayinmu na ‘yan adam, mu hukumar sufurin jiragen ƙasa muna nan muna aiki tuƙuru ba dare ba rana kan ganin irin hakan ba ta sake faruwa ba, kuma da yardar Allah hakan ba za ta sake kasancewa ba. ɗaya daga cikin matakan kuwa idan ka lura a cikin jirgin yanzu haka akwai ‘yan sanda a ciki, kuma akwai jami’an farin kaya a ciki. Kuma a hanyar ma an tanadi tsaro, domin duk wani fasinja da yake shiga jirgin zai tabbatar maka duk wani siteshon da za ka tarar akwai sojoji suna nan don bayar da tsaro. Baya ga duk waɗannan muna da ‘yan sa-kai, waɗanda su ma suna taimakawa ta wannan ɓangare na bayar da tsaro ga jirgin. Duk da cewa hatsarin ba wai ya shafi waɗannan ba ne, tsautsayi ne kawai ya samu, Allah ya kawo. A taƙaice dai abinda zan iya cewa kwarai da gaske muna alfahari da ƙoƙarin da ma’aikatanmu ke yi dare da rana na ganin komai ya tafi yadda ake buƙata.

Akwai wani ɗaki da shi MD ya nuna mana wanda ƙwarai ya ja hankali ta yadda za ku iya sa-ido kan jirgin tun daga tashin sa har zuwa sauka, wato wani talabijin da ke haska jirgin daga tashinsa har isar sa. Ko za ka yi wa masu karatunmu ƙarin bayani game da shi?

Lallai akwai abinda muke cewa ‘control room’ da Turanci, wanda ake bin didigin zirga-zirgar jiragen. Wanda idan mutum na wurin duk abinda ke gudana a hanyar tafiyar zai iya gani, hakan zai iya ba ka damar ganin komai zai samu jirgin ba wai sai an kira an sanar ba. Kuma baya ga gani ɗin ma, za a iya magana da jirgin, ma’ana dai jirgin yana tafiya daidai da cigaban da zamani ya kawo na sawwaka abubuwa ta fuskoki da dama. Wannan cigaba da zamani ya zo da shi da muke amfani da shi, da zaran jirgin ya tashi daga nan, zai dinga nuna ma duka halin da yake ciki har gudun da yake yi, har sai ya isa masaukinsa na Rigasa a Kaduna. Bugu da ƙari wannan cigaba na ƙari da aka samu a sawun tafiyar jirgin ba nan muke fatan tsayawa ba, domin yanzu haka akwai abinda shi MD yake ƙoƙari, ko yanzu da ku ka zo kun ji ya je wani workshop. Yana fafutukar ganin an samu wani tarago an tada, wanda idan Allah ya yarda nan da wata ɗaya ko biyu za mu samar da wata tarago. Dama haka muka saba, wata tarago daga Kaduna, wata kuma daga Abuja. Ta yadda wanda ya kwaso fasinja daga Kaduna zai kama hanyarsa, shi ma na Abuja haka, saidai su haɗu a Kubuwa ko kuma a Jere. Ka ga kuwa wannan babban cigaba ne da zai ƙara yawan tafiye-tafiye da ƙarin fasinjoji. Ma’ana daga uku ɗin da mu ke yi yanzu a cikin kwana huɗu, za mu dawo muna huɗu, za mu ma iya ƙara shi har zuwa shida da yardar Allah. Duk wannan ƙoƙarin da MD ya ke ta fafutukar ganin an cimmawa kenan.

Mun gode.

Ni ma na gode.

By ukarofi