
A ranar Alhamis Sakataren walwala na jam’iyyar APC a Jihar Kano, Bashir Tijjani Maisango, ya yi murabus daga jam’iyyar inda ake sa ran zai koma jam’iyyar ADC.
Maisango, wanda a baya ya riƙe mukamin mataimakin sakatare a jam’iyyar, na daga cikin manyan jagorori masu tasiri da kuma masu jan hankalin jama’a a matakin kasa a Kano.
A cikin wasiƙar murabus ɗinsa mai taken “Murabus na radin kai daga jam’iyyar APC” wadda ya aikewa shugaban jam’iyyar na jiha, ya bayyana godiyarsa ga jam’iyyar bisa damar da ta ba shi a lokacin da yake cikinta.
Ya ce: “Ni, Bashir Tijjani Maisango, ina sanar da murabus na daga jam’iyyar APC daga ranar 1 ga Afrilu, 2026.
“Ina godiya da damar da jam’iyyar ta ba ni, kuma ina yi mata fatan alheri.”
Majiyoyi sun bayyana cewa Maisango ya dauki matakin ne domin nuna goyon baya ga tsohon mataimakin gwamnan jihar, Nasiru Gawuna, wanda ya fice daga jam’iyyar a ranar 30 ga Maris.
Har ila yau, an rawaito cewa ana sa ran Maisango zai yi rajista da jam’iyyar ADC a mazabarsa ta Dakata da ke Kano.
