EFCC na ƙoƙarin tabbatar da ƙwace kadarori 57 da aka danganta da Malami

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta nemi wata babbar kotu da ta bayar da umarnin ƙwace wasu kadarori guda 57 da ake danganta su da tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami, har abada.

EFCC ta ce, an shigar da wannan buƙata ne ƙarƙashin Sashe na 17 na dokar Advance Fee Fraud and Other Fraud-Related Offences Act, 2006, inda hukumar ta bayyana kadarorin a matsayin waɗanda ake da ƙwarin gwiwar zargin cewa sun samo asali ne daga haramtattun ayyuka.

Hukumar ta jaddada cewa binciken da ta gudanar ya nuna alamun cewa kadarorin na iya kasancewa sakamakon ayyukan da suka saɓa wa doka, don haka take neman kotu ta tabbatar da kwace su gaba ɗaya.

Ana sa ran kotun za ta yanke hukunci kan wannan buƙata a kwanaki masu zuwa, lamarin da ka iya ƙara ɗaga ƙura a fagen siyasa da shari’a a Nijeriya.

Wani masanin harkar shari’a da ke da masaniya akan shari’ar ya ce EFCC ta samu ƙorafe-ƙorafe da fama akan tsohon antonin daga ƙungiyoyi mabanbanta da ke zargin sa da hannu a rashawa, saɓa wa dokokin aiki da badaƙala.

By Babaji