Ministan Sufuri ya yi murabus don fitowa takarar Gwamnan Gombe

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Ministan Sufuri Sanata Sa’idu Ahmed Alkali, ya ajiye muƙaminsa domin fitowa takarar Gwamnan Jihar Gombe.

Da haka ya shiga jerin jami’an Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Tinubu da suka ajiye mukamansu domin neman takara a zaben shekarar 2027.

Ya ajiye mukamin nasa ne sa’o’i kadan kafin cikar wa’adin da shugaban kasa ya ba wa jami’an gwamnatinsa da ke da muradin tsayawa takara su ajiye mukaminsu.

Sauran ministocin da suka ajiye mukamansu sun hada da Ministan Harkokin Waje, Ahmed Tuggar, wanda ke neman fitowa takarar Gwamnan Jihar Bauchi da kuma Karamin Minista, Sununu da ke son fitowa takarar dan majalisar dokoki ta kasa a Jihar Kebbi.

A wata sanarwa da kakakin ministan, Umar Alkali Jibril, ya fitar a ranar Talata, ya ce ministan ya nuna godiya ga Shugaba Tinubu bisa damar da ya ba shi na yin hidima, tare da jaddada ci gaba da aka samu a fannin sufuri a lokacin da yake kan mukami.

Sanarwar ta ƙara da cewa Shugaban ƙasa ya amince da murabus ɗin, tare da gode masa bisa jajircewa da hidimar da ya bayar wa ƙasa.

By ukarofi