Yadda sulhun da Pantami ya yi tsakanin El-Rufai da Uba Sani ya janyo cece-kuce

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

’Yan Nijeriya na ci gaba da tafka muhawara musamman a shafukan sada zumunta game da sulhu da fitaccen malamin Addinin Musulunci Sheikh Ali Isa Pantami ya yi wa El-Rufai da Uba Sani.

Al’amarin ya ɗauki hankalin mutane da dama musamman waɗanda ke bibiyar abubuwan da suka shiga tsakanin tsohon gwamna da gwamnan jihar na yanzu.

Mutanen biyu dai sun jima ba sa ga maciji da juna, sakamakon rashin jituwa da ta shiga tsakaninsu, jim kaɗan bayan saukar El-Rufai daga mulkin jihar Kaduna.

Malamin ya yi musu sulhu ne a lokacin jana’izar mahaifiyar El-Rufai, Hajiya Umma ranar Lahadi a Abuja.

Hajiya Umma El-Rufai ta rasu ne ranar Juma’a bayan fama da jinya a birnin Alƙahira da ke Masar.

Dattijuwar ta rasu ne a daidai lokacin da El-Rufai ke tsare a hannun hukumar ICPC mai yaƙi da almundahanar kuɗaɗe, wani abu da ya ƙara ɗaukar hankalin yan ƙasar da dama. Sai dai hukumar ta sake shi jim kaɗan bayan ɓullar labarin rasuwar mahaifiyar tasa.

Kasancewar mutanen biyu sun jima da samun rashin jituwa tsakaninsu, Sheikh Pantami ya yi amfani da damarsu a wurin jana’izar wajen yi musu sulhun a bainar jama’a.

Jim kaɗan bayan binne gawar a maƙabarta, bayan mutane sun fara gaisawa, sai malamin ya fara yin nasiha ga mahalarta janazar, wadda daga baya ta rikiɗe ta koma sulhu tsakanin El-Rufai da Uba Sani, waɗanda ke tsaye kusa da juna, shi kuwa malamin na tsakiyarsu.

Ya fara da batun haɗin kai tsakanin al’ummar Musulmai, yana mai cewa ya kamata musulmai su riƙa ganin alkhairan juna.

“Mu tuna da alkhairan juna fiye da sharrin juna, mu sani abin da haɗa mu, ya fi abin da raba mu yawa’.’

Ya ci gaba da cewa, “mu sani da ni da kai duk abin da muke so ba wanda zai ba mu shi sai Allah, ba kuma wanda zai iya hana mu sai Allah.”

Daga nan sai ya kama hannun Uba Sani – da ke ɗaya ɓarin nasa, ya kuma kama na El-Rufai da ke ɗaya gefen – ya ce musu ku yafi juna.

Ya sanya su suka gaisa da juna ”don Allah a yafe wa juna, a kama hannun juna, gaba ta fi baya baya yawa, a yafe wa juna Allah ya yafe mana gaba ɗaya, sai ya kalli El-Rufai ya ce your Eɗcellency an yafe ko”.

Sai El-Rufai ya ɗaga kai alamun ya amince, sai Sheikh Pantami ya ce ”yawwa an yafe wa juna”, sai mutanen da ke wurin suka yi kabbara.

Tun bayan yin wannan sulhu mutane suka riƙa tafka muhawara kan ko sulhun zai ɗore, ganin yanayin da lokaci da kuma wurin da aka yi shi.

By ukarofi