NCC ta umarci kamfanonin sadarwa su biya kwastomomi diyya kan matsalar sabis

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Sadarwa ta ƙasa (NCC), ta umarci kamfanonin sadarwa na wayar hannu da su biya kwastomominsu diyya idan aka samu gazawar ingancin sabis a wurare da lokuta da aka ƙayyade.

A cikin wata sanarwa da Sashen Hulɗa da Jama’a na hukumar ya fitar, NCC ta bayyana cewa bai kamata kwastomomi su ɗauki nauyin matsalolin da ke tasowa daga gazawar kamfanoni wajen cika ƙa’idojin sabis ba.

Don haka, duk kamfanin da ya gaza cika ƙa’idojin inganci, zai biya diyya kai tsaye ga masu amfani da sabis ɗinsa.

Sanarwar ta ƙara da cewa, diyya za ta shafi lokutan da aka samu raunin sabis, musamman idan hakan ya saɓa wa ƙa’idojin kimanta inganci (ƙuality of Serɓice – ƙoS). Za a bai wa kwastomomi wannan diyya ne ta hanyar ƙarin kuɗin kira (airtime), wanda za a lissafa bisa yadda suke kashe kuɗi a baya, tare da la’akari da yankunan ƙananan hukumomi da aka samu matsalar sadarwar.

Hukumar ta jaddada cewa wannan mataki wani ɓangare ne na manufofinta na mayar da hankalin tsari da dokoki kan kare muradun masu amfani da sabis.

Ta ce, a yau, harkokin sadarwa sun zama ginshiƙi ga tattalin arziki, hulɗar jama’a, da samun damar fasahar zamani. Don haka duk wani tangarɗa a sabis na iya shafar aiki, kasuwanci da kuma amincewar jama’a da tsarin sadarwa gaba ɗaya.

NCC ta kuma bayyana cewa duk da cewa a baya tana amfani da tara domin ladabtar da kamfanonin da suka gaza, yanzu tana ƙara karkata akalar tsari zuwa kare haƙƙin kwastomomi kai tsaye, tare da ƙarfafa ɗaukar alhaki a cikin masana’antar sadarwa.

Bugu da ƙari, hukumar ta umurci kamfanonin hasumiyar sadarwa (Tower Companies) da ke samar da muhimman kayayyakin more rayuwa kamar turakun sadarwa, da su zuba jari sosai wajen inganta kayan aiki da sabis, musamman ta hanyar amfani da kuɗaɗen tarar da aka ƙwace daga gare su da sauran matakan hukunci.

Hukumar ta kuma yi alƙawarin ci gaba da saka ido tare da ƙarfafa kamfanonin sadarwa su zuba jari a inganta ƙarfin cibiyoyin sadarwa, faɗaɗa damar aiki, da kuma sabunta kayan aiki domin biyan buƙatun jama’a da ke ƙaruwa.

A ƙarshe, NCC ta jaddada cewa za ta ci gaba da amfani da dukkan hanyoyin doka domin tabbatar da gaskiya, adalci da riƙon amana a fannin sadarwa, tare da tabbatar da cewa kowane ɗan ƙasa ya samu ingantaccen sabis kamar yadda ya cancanta.

By ukarofi