
Hukumar Zaɓe Ƙasa INEC, ta umarci Kwamishinonin zaɓe na jihohi (RECs) da su dakatar da duk wani shiri da tallace-tallace da suka shafi shirin sake tantance masu kada kuri’a a fadin kasar nan.
Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da tattaunawa kan yadda za a inganta tsarin rajistar masu kada kuri’a da kuma tabbatar da sahihancin bayanan masu zabe kafin babban zaben kasa mai zuwa.
A cewar majiyoyi daga cikin hukumar, an umurci dukkan ofisoshin INEC na jihohi da su dakatar da duk wani shiri da aka fara domin gudanar da wannan aikin, har sai an bayar da sabbin umarni daga hedikwatar hukumar.
Rahotanni sun nuna cewa, wannan dakatarwa na iya kasancewa sakamakon wasu sabbin tsare-tsare da hukumar ke nazari a kai, domin kaucewa rudani ko matsaloli da ka iya tasowa yayin gudanar da aikin.
Masu ruwa da tsaki a harkar zabe na kallon wannan mataki a matsayin wani yunkuri na sake tsara tsarin domin tabbatar da gaskiya da adalci a zabukan Najeriya.
Ana sa ran hukumar za ta sake bayyana sabuwar rana ko tsarin da za a bi wajen aiwatar da shirin nan gaba domin inganta lamuran masu zaɓe a Nijeriya.
