Billiri da Balanga sun mara wa Ali Isa baya a zaɓen 2027

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe

Al’ummomi daga mazaɓar tarayya ta Billiri da Balanga a Jihar Gombe sun bayyana cikakken goyon bayansu ga wakilinsu a majalisar wakilai ta ƙasa, Hon. Ali Isa JC, inda suka yaba da irin gudunmawar da yake bayarwa da kuma ayyukan raya ƙasa da ya aiwatar.

An bayyana wannan yabon ne yayin bikin ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka da ɗan majalisar ya aiwatar a garuruwan Buwangal da Jessu.

Da yake jawabi a wajen taron, tsohon ɗan majalisar wakilai daga mazabar, Hon. Yusuf Manu Swa, ya jinjinawa nasarorin da Ali Isa ya samu, inda ya bayyana aikinsa a matsayin abin koyi da kuma mai tasiri.

Ya amince cewa ko a lokacin da yake kan mulki bai samu damar aiwatar da irin waɗannan ayyuka ba, yana mai cewa Ali Isa ya yi fice a fannoni daban-daban a ƙananan hukumomin Billiri da Balanga.

“Mun gamsu da ayyukansa, kuma muna roƙonsa da ya ci gaba da wakiltar mu bayan 2027,” in ji Manu Swa.

Ya kuma yaba da salon shugabancin sa na haɗa kan jama’a, yana mai nuni da yadda ya iya haɗa mutane daga ƙabilu, addinai da jam’iyyu daban-daban duk da kasancewarsa Bafullace daga Cham a ƙaramar hukumar Balanga.

A nasa jawabin, Sarkin Cham, Ndu Gram Cham, James Chachis, ya bayyana Ali Isa a matsayin ɗan siyasa na gari wanda ya kawo sauyi mai ma’ana a wakilci a mazaɓar.

Ya kuma yaba da yadda ɗan majalisar ke kasancewa kusa da jama’a da kuma sauraron buƙatunsu.

Da yake nasa jawabin, Hon. Ali Isa JC ya jaddada cewa manufarsa ita ce yi wa al’umma hidima, yana mai cewa dukkan ayyukan da ya aiwatar sun ta’allaƙa ne da buƙatun jama’arsa.

“An zaɓe ni ne domin in yi wa jama’a hidima, ba domin in mulke su ba. Duk abin da na yi, na yi ne bisa ga buƙatu da fifikon al’ummata,” in ji shi.

Ya bayyana wasu daga cikin ayyukan da ya aiwatar, ciki har da gina makarantu, cibiyoyin lafiya, masallatai da coci-coci, tare da shirye-shiryen tallafa wa mata da matasa.

Ya ƙara da cewa an gina hanyoyi da dama a mazabar, yayin da mutane da dama suka samu aikin dindindin na albashi ta hanyar ƙoƙarinsa.

A matsayin karramawa ga irin gudunmawar da yake bayarwa, sarakunan yankuna daga Jessu, Nyuwar da Wala Lunguda sun naɗa masa sarautu daban-daban.

Daga cikin ayyukan da aka ƙaddamar a wajen taron akwai sabon masallacin Juma’a a Buwangal, coci a Jessu, da kuma amincewa da gina asibiti a yankin.

Al’ummomin sun sake jaddada goyon bayansu ga Ali Isa JC, tare da bayyana shirinsu na mara masa baya a zaɓen 2027, bisa la’akari da irin nasarorin da ya samu da kuma karɓuwar da yake da ita a tsakanin jama’a.

By ukarofi