Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Cibiyar nazarin harsunan Nijeriya fassara da hikimomin al’umma tare da haɗin gwiwar School of Oriental and African Studies (SOAS) sun shirya taron yini guda kan “Inganta Makomar Afirka Ta Hanyar Fassarar Adabi” da ya gudana a Jami’ar Bayero Kano.
A jawabin buɗe taron mai taken “Fassarar Adabi a Matsayin Ginshikin Al’adu da Tattalin Arziki,”
Wanda Dakta Ida Hadjivayanis ta jaddada muhimmancin fassarar adabi wajen kare al’adu, ƙarfafa fahimtar juna tsakanin al’umma da kuma samar da damarmakin tattalin arziki ta fuskar wallafe-wallafe da masana’antar ƙere-ƙere.
A nasa jawabin shugaban cibiyar nazarin harsunan Nijeriya fassara da hikimomin al’umma, Farfesa Yakubu Magaji Azare ya bayyana cewa wannan yunƙuri ya samo asali ne bayan tattaunawar da aka yi yayin ziyarar sa zuwa jami’ar SOAS a Landan, inda aka fahimci cewa akwai buƙatar bunƙasa nazarin adabi da fassara a Afirka.
Ya ce a faɗin duniya, fassara ta taimaka wajen fahimtar yadda al’ummomi daban-daban ke rayuwa, al’adunsu, tsarin zamantakewarsu da cigaban su. A cewarsa, duk da cewa an rubuta dubban littattafai a harshen Hausa, yawancinsu sun tsaya ne a cikin al’ummar Hausawa saboda ba a fassara su zuwa wasu harsuna ba.
Farfesa Azare ya bayyana cewa fassara littattafan Hausa zuwa wasu harsuna zai bai wa sauran al’ummomin duniya damar fahimtar al’adun Hausawa, rayuwarsu da tsarin zamantakewar su.
Ya ƙara da cewa bunƙasa fassarar adabi zai kuma ba da damar fassara littattafan wasu harsuna zuwa Hausa, lamarin da zai ƙarfafa musayar ilimi da hulɗar al’adu.
Ya ƙara da cewa tun tarihi, fassara ta taka muhimmiyar rawa wajen yaɗa ilimi da wayewa, domin al’umma da dama sun dogara da ita wajen samun damar karanta littattafan kimiyya, adabi da falsafa daga wasu al’ummomi.
Farfesa Azare ya jaddada cewa babban maƙasudin taron shi ne samar da haɗin kai tsakanin masu fassara, marubuta da masu ɗab’i. Ya bayyana cewa masu fassara na buƙatar masu ɗab’i da za su buga ayyukansu su kuma kai su kasuwa, yayin da marubuta ke buƙatar ƙara ƙwarewa wajen rubuta ayyuka masu amfani ga al’umma.
A cewarsa, masu ɗab’i ma suna da rawar takawa wajen gano hanyoyin da za su kai ayyukan marubuta da masu fassara kasuwa domin ƙarfafa al’adar karatu da kuma sauƙaƙa samun littattafai ga jama’a.
Sai dai ya nuna damuwa kan yadda al’adar karatu ke raguwa, yana mai cewa yawaitar amfani da kafafen zamani ya sa mutane da dama sun rage ɗaukar littattafai suna karantawa.
Ita ma da take jawabi a taron, Dr. Carmen McCain, wadda aka fi sani da Talatu, ta ce akwai buƙatar a riƙa fassara ayyuka daga harsunan duniya zuwa Hausa.
Ta ce yayin da Dr. Ida Hadjivayanis ke gudanar da fassara daga Turanci zuwa Swahili, ya kamata a samu irin wannan ƙoƙari a Hausa saboda yalwar harshen da kuma karɓuwar sa.
Dr. McCain ta ce, ƙara yawan fassara zuwa Hausa zai taimaka wajen faɗaɗa samun ilimin duniya tare da ƙarfafa matsayin harshen Hausa a fannonin adabi da ilimi.
Mahalarta taron sun haɗa da masu fassara, marubuta, masu dab’i da sauran masu ruwa da tsaki a harkar fassara. Masu lura da al’amura na ganin cewa taron wanda shi ne na farko, ana sa ran ya zama sabon yunƙuri da zai kawo sauyi a harkar fassara da wallafe-wallafe a Arewacin Nijeriya da ma sauran sassan duniya.
