
Farashin ɗanyen mai ya fadi ƙasa da dala 95 a kowace ganga a ranar Laraba, 8 ga watan Afrilu, 2026, bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta makonni biyu tsakanin Amurka da Iran.
Rahotanni sun nuna cewa farashin man nau’in Brent ya sauka da kusan kashi 13 cikin ɗari zuwa dala 94.76, yayin da nau’in WTI ya koma kusan dala 96.
Wannan ragi ya biyo bayan sanarwar da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi na dakatar da hare-hare na tsawon mako biyu, muddin Iran ta buɗe Mashigar Hormuz wadda ita ce hanyar da kashi ɗaya bisa biyar na man duniya ke bi.
Hakan ya rage fargabar yaƙi a kasuwar mai, inda farashin ya sauko daga sama da dala 110 zuwa dala 130 da ya kai a makonnin baya.
Sai dai masana na gargaɗin cewa zaman lafiyar na iya zama na wucin gadi ne saboda har yanzu akwak taƙddama a wasu sassan yankin.
A Najeriya, ana sa ran farashin mai zai ragu kaɗan daga yadda yake a yanzu (kusan N1,370 kan kowace lita).
Wannan na zuwa ne bayan rahoton Bankin Duniya na watan Afrilu da ya nuna cewa farashin man fetur a ƙasar ya ƙaru da sama da kashi 50 tun bayan fara yaƙin Iran da Amurka kusan mako biyar da suka wuce, abin da ya haifar da tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki.
