Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kaduna ta bayar da belin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a shari’ar cin hanci da rashawa da Hukumar ICPC ke tuhumarsa da ita.
Rahotanni sun bayyana cewa alkalin kotun, Mai shari’a Rilwanu Aikawa, ne ya yanke hukuncin a ranar Talata, bayan da ya ɗage sauraron ƙarar daga ranar 1 ga Afrilu zuwa 14 ga Afrilu, 2026 domin nazarin hujjojin ɓangarorin biyu.
Kotun ta amince da bayar da belin kan kuɗi Naira miliyan 200, amma ta umarci cewa El-Rufai zai ci gaba da kasancewa a hannun ICPC har sai ya cika dukkan sharuɗɗan belin.
Daga cikin sharuɗɗan, an hana shi yin magana a bainar jama’a game da shari’ar, tare da wajabta masa halartar duk zaman kotu.
Lauyan El-Rufai, Ubong Akpan, ya ƙi yin tsokaci ga manema labarai bayan kammala zaman kotun.
Sai dai wani na kusa da tsohon gwamnan, Hayatudeen Lawal Makarfi, ya bayyana cewa kotun ta sanya kusan sharuɗɗa guda 10, ciki har da samar da mai tsaya masa (surety) mai kadarar fili da kuma mai sarauta.
ɗansa, Bello El-Rufai, ya tabbatar da cewa an bai wa mahaifinsa beli.
A ranar Talata ɗin ma, El-Rufai ya gurfana a gaban wata Kotun Jihar Kaduna kan wata dabam buƙatar beli a wani ƙarin shari’a, amma alkalin kotun, Darius Khobo, ya ɗage yanke hukunci zuwa ranar 21 ga Afrilu, 2026.
A ranar Litinin, ICPC ta gurfanar da El-Rufai a kan sabbin tuhume-tuhume guda tara da suka shafi zargin damfara da cin zarafin ofis. Hukumar ta cire sunan Amadu Sule daga cikin sabuwar takardar tuhuma.
Daga cikin zarge-zargen, ICPC na cewa El-Rufai ya sa Gwamnatin Jihar Kaduna ta fitar da kusan Naira biliyan 11 ga wata ƙungiya da ba a yi mata rajista ba domin aikin layin dogo na birni (light rail) wanda ba a aiwatar ba.
Haka kuma, ana zarginsa da amincewa da karɓar kusan Naira miliyan 289.8 a matsayin kuɗin sallama daga aiki (seɓerance allowance), wanda ya zarce adadin da doka ta tanada na kusan Naira miliyan 20.
A wani zargi, an ce ya yi almundahana da sama da dala miliyan 1.08 daga cikin rancen Bankin Duniya da aka bai wa jihar, wanda ya saba yarjejeniyar rancen.
Har ila yau, ana zarginsa da haɗa baki da wani mutum da ke waje domin bayar da cin hanci ga jami’an bincike na tarayya don karkatar da bincike da ake yi.
Sauran tuhume-tuhumen sun haɗa da ba da kwangilar CCTɓ ta Naira biliyan 4.6 a Kaduna ba bisa ƙa’ida ba, da kuma bai wa wani na kusa da shi gata a cikin wannan kwangila.
Haka kuma, ana zarginsa da cin zarafin ofis a harkar filaye, ciki har da karɓe da sake bai wa wasu filaye a hanyar Kaduna zuwa Zariya domin amfanar da wasu kamfanoni masu alaƙa da shi.
Sai dai El-Rufai ya musanta dukkan zarge-zargen da ake masa.
Tun daga ranar 19 ga Fabrairu, El-Rufai ke tsare a hannun ICPC bayan EFCC ta sake shi. An kuma ba shi damar fita na ɗan lokaci a ranar 27 ga Maris domin halartar jana’izar mahaifiyarsa.
Da yake martani, Bello El-Rufai ya nuna farin ciki da hukuncin belin, yana mai gode wa manema labarai, lauyoyi da masu goyon baya.
Ya kuma gargadi kafafen yaɗa labarai da su guji yin hasashe kan shari’ar, yana mai cewa akwai bambanci tsakanin ra’ayin jama’a da kuma hukuncin shari’a.
Wani lauya a Kaduna, El-Zubair Abubakar, ya bayyana cewa El-Rufai ba zai samu ‘yanci nan take ba duk da belin, saboda akwai wasu shari’o’i guda biyu da ake yi masa a kotuna daban-daban.
Ya ce duk da cewa Kotun Tarayya ta ba shi beli, dole ne ya cika sharuɗɗan kafin a sake shi, kuma hakan ya shafi wannan shari’ar kawai.
A cewarsa, akwai wata shari’a a Kotun Jihar Kaduna wadda har yanzu ba a ba shi beli ba, wanda hakan ke nufin zai ci gaba da kasancewa a tsare har sai an yanke hukunci a can ma.
Ya ƙara da cewa, ana sa ran za a ba shi beli a wannan shari’a ta biyu, domin irin waɗannan laifuka yawanci ana bayar da beli a kansu a dokar Nijeriya.
