Kotun Ƙoli ta ɗage shari’ar Masarautar Kano zuwa Afrilun 2027 bayan gabatar da sabon ƙorafi

Spread the love

Kotun Ƙoli ta ayyana ranar 19 ga watan Afrilun 2027 domin cigaba da sauraren ƙarar da Alhaji Aminu Babba Ɗan Agundi ya shigar, inda yake kalubalantar hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara da ta ce ba shi da hurumin shigar da ƙara akan batun cire Aminu Ado Bayero daga sarautar Kano.

A zaman kotun na yau Litinin, lauyan mai ƙara ya gabatar da roƙonsa a gaban alkalai ba tare da wata turjiya daga sauran lauyoyin da ke kare waɗanda ake ƙara ba. Sai dai lauyan Majalisar Dokokin Jihar Kano, Barista Bashir Yusuf Tudun Wuzirci, ya nemi ya nuna adawa, amma kotun ta bayyana cewa lokacin yin hakan ya riga ya wuce.

Daga ƙarshe, kotun ta ɗage shari’ar na tsawon shekara guda domin bai wa ɓangarorin damar ci gaba da gabatar da hujjojinsu.

Tun da farko, Alhaji Aminu Babba Dan Agundi ne ya shigar da ƙarar a Kotun Tarayya da ke Kano, inda ya kalubalanci matakin da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta ɗauka na cire Aminu Ado Bayero daga sarautar Kano. Ya bayyana cewa yana da hurumin shigar da ƙarar a matsayinsa na ɗaya daga cikin masu naɗa sarki, kuma kotun ta amince da matsayinsa.

Sai dai waɗanda aka shigar da ƙarar a kansu sun ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ɗaukaka Ƙara, wadda ta soke hukuncin Kotun Tarayya tare da cewa bai da hurumin shigar da ƙarar. Wannan ne ya sa ya sake garzayawa Kotun Koli domin neman hukunci na ƙarshe.

Shari’ar na da alaƙa da rikicin masarautar Kano wanda ya daɗe yana jawo cece-kuce a tsakanin al’umma da masu ruwa da tsaki. Ana sa ran kowanne ɓangare zai gabatar da cikakkun hujjoji a gaban Kotun Koli domin tabbatar da matsayinsa bisa doka.

Masana harkokin shari’a na ganin cewa hukuncin da Kotun Koli za ta yanke zai yi tasiri sosai ga tsarin masarautun gargajiya da kuma yadda doka ke tafiyar da irin waɗannan batutuwa a Nijeriya.

By Babaji